Matasa Sun Tura Saƙo ga Bola Tinubu da 'Yan Bindiga Suka Ƙona Garuruwa 7 a Jihar Neja

Matasa Sun Tura Saƙo ga Bola Tinubu da 'Yan Bindiga Suka Ƙona Garuruwa 7 a Jihar Neja

  • Matasan Borgu sun yi iƙirarin cewa ‘yan bindiga sun ƙone fiye da ƙauyuka da garuruwa bakwai a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya
  • Sun bayyana cewa har yanzu akwai mutane da dama da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan hare-haren da aka kai
  • Matasan sun roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Mohammed Bago da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Matasan masarautar Borgu da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Agwara da Borgu a jihar Neja sun koka kan tabarbarewa tsaro a yankinsu.

Matasan sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun ƙone fiye da ƙauyuka da garuruwa bakwai, yayin da mutane da dama daga yankin ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane.

Jihar neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban Ƙungiyar Matasan Masarautar Borgu, Kwamared Abdullahi Yahaya Saudaki, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ƙarshen mako, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Har da talauci: An gano abubuwa 3 da ke kara yaduwar cutar HIV

Kwamared Sadauki ya ce matsalar rashin tsaro na ci gaba da yaɗuwa zuwa sauran garuruwan da ke karkshin masarautar Borgu.

Yan bindiga sun lalata kauyuka a Neja

Saudaki ya ce ɓarnar da rashin tsaro ya haddasa ta yi muni, inda rayuka suka salwanta, iyalai da dama suka rasa matsugunansu, sannan ƙauyuka da garuruwa da dama suka ƙone ƙurmus.

Ya lissafa wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa da suka haɗa da Konkoso, Kasuwan Daji, Pissa, Gangale, Woro, Tungan Makeri, Old Gangale, Boiya, Bakinba da Wawa.

Ya ce manoma sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron hare-haren yan bindiga, lamarin da ya durƙusar da harkokin noma da kasuwanci tare da jefa tattalin arzikin yankin cikin mawuyacin hali.

Makarantu da asibitoci sun daina aiki

Shugaban matasan ya ce yara ba sa iya zuwa makaranta cikin kwanciyar hankali, inda ya bayyana cewa makarantu da ke New Bussa da kewaye kaɗai ne ke aiki, yayin da sauran aka rufe su tun watan Janairun 2026.

Sadauki ya ƙara da cewa ayyukan kiwon lafiya ma sun tsaya cak, yayin da al'ummar yankin ke rayuwa cikin fargabar hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya tirje, ya yi magana kan sulhu da ƴan bindiga a Zamfara

Shugaba Tinubu da Bago.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Sun roƙi Tinubu da Bago su ɗauki mataki

Ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kira Jagaban Borgu, da Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Saudaki ya kuma buƙaci a ƙarfafa tattara bayanan sirri domin inganta kariyar al'ummomin karkara daga hare-haren miyagun yan ta'adda, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Sojoji sun yiwa yan bindiga luguden wuta

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin sama da ke karkashin Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta'adda da dama a jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin sojoji ya kai wadannan hare-haren ne bayan samun bayanan sirri masu inganci, wadanda ke nuna 'yan bindiga kimamin 200 na tafiya a kan babura.

Bayan kashe da dama daga cikin yan bindigar, an kuma lalata wani wurin da ake zargin suna tara kayayyaki da man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262