Kotu Ta Shirya Hukunci a Shari'ar da Hukumar EFCC Ta Nemi Kwace Kadarorin Malami

Kotu Ta Shirya Hukunci a Shari'ar da Hukumar EFCC Ta Nemi Kwace Kadarorin Malami

  • Babbar Kotun Tarayya ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar hukumar EFCC ta kwace kadarorin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami
  • EFCC ta ce tana zargin kadarorin guda 57 an mallake su ne ta haramtacciyar hanya don haka akwai bukatar karbe su
  • Lauyoyin tsohon ministan sun yi fatali da bukatar, sun ce hukumar ta dogara ne kan zato ba tare da gamsassun hujjoji ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage yanke hukunci kan ƙarar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar kan kadarorin da ake alakantawa da Abubakar Malami.

Kotun ta shirya yanke hukunci kan bukatar EFCC ta neman kwace kadarori 57 da ake zargin na tsohon Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami ne.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Abubakar Malami.
Tsohon ministn shari'a kuma dan takarar gwamnan Kebbi na ADC, Abubakar Malami a harabar kotu Hoto: Abubakar Malami
Source: Facebook

The Cable ta ce an saurari shari'ar ne a ranar Litinin a gaban Mai Shari'a Joyce Abdulmalik, wadda tun farko ta sanya ranar yanke hukunci bayan ɓangarorin biyu sun kammala gabatar da hujjojinsu.

EFCC ta nemi a kwace kadarorin

EFCC na roƙon kotu da ta ba da umarnin kwace kadarorin gaba ɗaya tare da mika su ga gwamnatin tarayya, tana mai cewa akwai dalilan da ke nuna cewa an same su ne ta hanyar ayyukan da suka saɓa wa doka.

A zaman da ya gabata, lauyan EFCC Jibrin Okutepa, ya buƙaci kotu ta amince da buƙatar, yana mai jingina da rantsuwar shaida mai sakin layi 47 da kuma hujjoji 46 da aka gabatar domin goyon bayan ƙarar.

Okutepa ya ce Malami da sauran waɗanda ake ƙara sun gaza bayyana sahihiyar hanyar da suka samu kadarorin, saboda haka ya roƙi kotu ta ba da umarnin kwace su har abada.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya

Lauyoyin Malami sun ce babu hujja

Sai dai lauyan Malami da sauran waɗanda ake ƙara, Adedayo Adedeji, ya buƙaci kotu da ta yi watsi da buƙatar EFCC tare da soke umarnin wucin gadi na kwace kadarorin da aka bayar a baya.

Adedeji, wanda ya dogara da rantsuwar shaidar Malami, ya ce ƙarar EFCC ta ginu ne kan zato ba tare da sahihan hujjoji ba.

EFCC.
Tambarin hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Ya ce:

"Kotu tana yanke hukunci ne bisa hujjoji, ba zato ba."

Ya kuma bayyana cewa EFCC ta dogara da bayanan da aka samu ba a cikin kotu ba, waɗanda ya ce dole ne a tantance su ta hanyar yi wa shaidu tambayoyi yayin shari'ar laifi.

Daga bisani, babbar kotun ta sanar da ɗage yanke hukunci zuwa ranar 10 ga watan Yuli, 2026, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kotu ta kwace N150m na dan Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kwace Naira miliyan 150 da ake dangantawa da dan Majalisar wakilai, Hon. Nicholas Mutu.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya rasa kadararsa bayan daurin shekaru 75 a gidan kaso

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a makon jiya.

A cewar hukumar, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan ta amince da bukatar EFCC na kwace kudin har abada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262