An Saki Bidiyon Bama Baman da Putin Ya Harba Babban Birnin Ukraine

An Saki Bidiyon Bama Baman da Putin Ya Harba Babban Birnin Ukraine

  • Rahoto ya bayyana cewa kasar Ukraine ta kasa kakkabo ko guda daga cikin manyan makamai masu linzami da Rasha ta harba
  • Sabon harin Rasha ya zo ne kwanaki kadan bayan harin da ya fi muni a bana, yayin da kasashen Turai da Amurka ke shirin zama
  • A bayanin da ta yi, Rasha ta sanar da cewa ta kai hari kan cibiyoyin soji da makamashi a Kyiv da yankunan da ke kewaye da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Russia - Rasha ta kai munanan hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan birnin Kyiv da sanyin safiyar Litinin.

Rashin isassun makamai masu kakkabo hare-hare da Amurka ta kera ya sa babban birnin Ukraine ke fuskantar matsala wajen kare kansa, kwanaki kadan bayan harin da ya fi muni a bana.

Kara karanta wannan

NYSC: Surutu yayi yawa minista ya canza magana game da sauyin khaki da adire

Shugaban Rasha, Vladimir Putin
Vladimir Putin a gefen hagu, wajen da aka kai hari Ukraine a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta wallafa cewa mummunan harin na dare ya zo ne gabanin taron kungiyar NATO da za a gudanar a Turkiyya a wannan makon.

Manyan hare-hare Rasha a Ukraine

Ma'aikatar Tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kai "gagarumin hari" kan Kyiv da wasu wurare ta amfani da makamai masu linzami masu dogon zango.

Ma'aikatar ta kuma ce an kai hari kan cibiyoyin soji da makamashi a Kyiv da yankunan da ke kewaye da ita, da kuma filayen jiragen saman soji a wasu yankunan Ukraine.

Rahotanni sun nuna cewa an ji jerin fashe-fashe a ciki da wajen Kyiv, yayin da kariyar sararin samaniyar Ukraine ke kokarin dakile jiragen sama marasa matuka na Rasha.

Mutane biyar sun mutu sannan 26 suka jikkata a yankin da ke kewaye da Kyiv, yayin da kuma aka kai hari kan tashar jiragen ruwa ta Odesa, inda akalla mutum daya ya jikkata, a cewar jami'an yankin.

Kara karanta wannan

An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi

Martanin sojojin kasar Ukraine

Sai dai rundunar sojin saman Ukraine ta ce ta kakkabo wasu makamai masu linzami 37 da kuma sama da kashi 90 cikin 100 na jiragen sama marasa matuka guda 351 da aka yi amfani da su wajen harin.

Zelensky ya sha cewa Ukraine na bukatar karin makaman kariya na tsarin Patriot da Amurka ta kera, wanda shi ne kadai makamin da kasar ke da shi da zai iya dakile makamai masu linzami na Rasha.

Zelensky ya nemi taimakon NATO

Shugaban Ukraine ya bukaci a dauki "matakai masu karfi" a taron NATO da zai fara ranar Talata a Ankara domin tabbatar da cewa Ukraine na iya kare kanta.

Ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Matukar makaman Patriot suna ajiye a rumbunan kawayen mu, Rasha za ta ci gaba da samun karfin gwiwar rusa gine-ginen gidajen jama'a."

Ya kara da cewa:

"Amurka da Turai suna da ikon dakatar da wannan ta'addanci."

Kara karanta wannan

Uba Sani: 'Yan sanda sun kama mutum 100 kan kisan Ummulkhairi a Kaduna'

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy
Volodymyr Zelenskyy a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yayin da ake ci gaba da aikin ceto har zuwa safiya, jami'an agajin gaggawa na ci gaba da neman mutanen da suka makale a cikin gine-ginen da hare-haren suka rusa.

Ga bidiyon barnar da aka yi a Ukraine da Al Jazeera ta wallafa a X:

Gobara ta tashi a Ukraine

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto muku cewa gwamnatin Ukraine ta tabbatar da cewa wata mummunar gobara ta tashi a wani yanki na kasar.

Bayanan da gwamnatin shugaba Volodymyr Zelenskyy ta fitar sun nuna cewa gobarar ta tashi ne bayan wasu hare-hare da Rasha ta kai.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng