Mubarak Mnisi: Yadda Dan Babban Fasto Ya Bar Kiristanci zuwa Musulunci
- Mubarak Mnisi wanda dan Afrika ta Kudu ne da mahaifinsa bishop ne a Cocin Zion, ya zama Musulmi na farko a danginsa
- Mahaifinsa ya yi tafiya daga nesa ya je gidansa a asirce don karbar kyautar Alqurani da Mubarak ya shirya masa a ranar haihuwarsa
- Mubarak ya bayyana cewa wani bidiyo na Musulunci ya da kasance yana gyarawa ne abin da ya jawo hankalinsa zuwa Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
South Africa - Mubarak Mnisi, wani bakar fata ta Musulmi a Afrika ta Kudu, ya bayar da labarin rayuwarsa mai ban mamaki a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli 2026, inda ya sanya hoto tare da mahaifinsa wanda ke sanye da kayan coci.
Kafi ya karbi addinin Musulunci, Mubarak ya ce ya girma a cikin Cocin Zion, inda mahaifinsa yake aiki a matsayin bishop shekaru da yawa.

Kara karanta wannan
Hadimin mataimakin shugaban majalisa ya yi murabus, ya koma bayan abokin hamayyarsa

Source: Facebook
Mubarak ya wallafa a Facebook cewa shi ne Musulmi na farko a duk danginsa, kuma ya bayyana yadda Allah Ya shiryar da shi zuwa Musulunci daga addinin da ya gada daga iyaye da kakanni.
Mahaifinsa ya karbi Kur'ani
A cikin sakonsa, Mubarak ya shaida wani abu da ya sosa masa zuciya sosai bayan ya shiga addinin Musulunci.
Ya ce mahaifin nasa ya yi tafiya mai nisa zuwa gidansa ba tare da sanar da shi ba, kawai don karbar kyautar Al-Kur'ani da aka fasara zuwa harshen isiZulu da Mubarak ya shirya masa a ranar haihuwarsa.
Lokacin da ya miqa masa Kur'anin, ya tuna da yadda shi ne na farko a dangin da ya rika riƙe Littafin Allah, kuma na farko da ya furta kalmar shahada.
Bidiyo ya jawo shi zuwa Musulunci
A cikin bayanan da ya yi, Mubarak ya kara da cewa mutane da dama sun taba tambayarsa dalilin da ya sa ya musulunta.
Amsar ta ce ya fara ne da wani bidiyo guda daya na Musulunci da yake aiki a kan shi a wajen da yake neman na tuwo.
Mubarak ya ce kafin ya fahimci ma'anar kalmomin Musulunci da ke cikin bidiyon, Allah Ya riga Ya shiga zuciyarsa yayin aikin sadarwa da yake yi.
Saboda haka ne ma ya ce ya kafa shiri na musamman da ake kira "House of Bilal Podcast" domin samar da kayan yaɗa labarai na Musulunci cikin harsunan Afrika ta Kudu da Ingilishi, domin wasu ma su sami damar gano Musulunci.

Source: Facebook
Mubarak ya kara da cewa kasancewa Baƙar fata dan Afirka ta Kudu Musulmi bai sa ya manta asalinsa ba, sai dai hakan ya nuna yana bin kyakkyawar hanya.
Sarkin Musulmi ya tara malamai
A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi zama da manyan malaman Arewacin Najeriya a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa malaman da suka halarci zaman sun hada da shugabannin kungiyoyin addinin Musulunci a fadin Najeriya.
Sarkin Musulmi ya tattauna batun zaman lafiya, matsalolin tsaro, rashin ilimi da abubuwan da suka addabi Arewacin Najeriya domin magance su.
Asali: Legit.ng
