Yaki Ya Koma Sabo: Iran Ta Jefa Bama Bamai kan Sansanonin Sojojin Amurka
- Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan hare-haren da sojojin Amurka suka kai a wasu sassan yankinsu ranar Laraba
- Sojojin Amurka sun bayyana cewa harin martani ne bayan Iran ta kai hari kan jiragen kasuwanci uku da ke bi ta mashigar Hormuz ranar Talata
- Wannan musayar wuta ta sake kamari yayin da Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait bayan farmakin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Kasar Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar da aka cimma domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.
Wannan na zuwa ne bayan sojojin Amurka sun kai hare-hare a Tehran da yankin mashigar Hormuz tare da dawo da takunkumin da ya shafi fitar da man fetur na Iran.

Source: Getty Images
Iran ta farmaki sansanonin sojin Amurka
Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan wurare sama da 80 a safiyar Laraba, suna mai cewa martani ne ga harin da Iran ta kai kan jiragen kasuwanci uku da ke bi ta mashigar Hormuz ranar Talata, in ji rahoton The Guardian.
A cikin wata sanarwa, babbar rundunar sojin Amurka ta ce Iran ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hari kan jiragen ruwa, ciki har da wani jirgin dakon iskar gas na Qatar.
Sai dai Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait.
Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kai hare-hare kan wurare 85, yayin da aka ji karar kararrawar gargadi a kasashen biyu. Sai dai babu rahoton barnar da aka tabbatar zuwa yanzu.
Hare-haren Amurka kan Iran
Wannan sabon rikici ya zo ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki tun watan Afrilu, da kuma yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da kasashen biyu suka sanya hannu a kai a watan da ya gabata domin ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da kawo karshen rikicin.
Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa hare-haren Amurka sun daki wuraren harba makamai, na'urorin kare sararin samaniya da cibiyoyin sa ido da ke gabar tekun Iran.
A gefe guda, kafafen yada labaran Iran sun ruwaito fashe-fashe a tsibirin Qeshm da kuma biranen Sirik da Bandar Abbas, kamar yadda rahoton AP News ya nuna.

Source: Getty Images
Sabon rikicin Iran da Amurka
Iran ta kuma zargi Amurka da maimaita karya yarjejeniyar fahimtar juna, tana mai gargadin cewa za ta dauki matakai masu tsauri.
Babban mai tattaunawar Iran da Amurka, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce daga cikin abubuwan da suka karya yarjejeniyar akwai matakin Amurka na dawo da takunkumin fitar da man fetur na Iran.
A watan da ya gabata ne Amurka ta sassauta takunkumin bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, amma ta sake dawo da shi ranar Talata bayan harin da aka kai kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Iran da Amurka sun cimma yarjejeniya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ce Amurka da Iran sun cimma yarjejeniya domin sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.
Kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Amurka da manyan kasuwannin Asiya sun yi tashin gwauron zabi, yayin da farashin mai ya faɗi.
Rufe mashigar Hormuz ya haifar da ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka taɓa addabar kasuwannin man fetur na duniya a tarihi.
Asali: Legit.ng

