'Yan ta'adda sun kai wa sojojin Nijar hari, sun halaka wasu

'Yan ta'adda sun kai wa sojojin Nijar hari, sun halaka wasu

A daren da ya gabata ne 'yan ta'adda suka kai hari wani sansanin jami'an tsaro da 'yan ta'addan suka dade suna harara a yankin Diffa.

Wata majiya ta tabbatar da cewa har yanzu ba a san yawan dakarun da suka rasa rayukansu ba, jarida The Punch ta ruwaito.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a Blabrine a ranar Litinin wurin karfe 11 na dare, kamar yadda wata kungiya mai suna Mara Mamadou ta sanar a Diffa.

Wani jami'in a yankin ya tabbatar da cewa 'yan bindiga ne suka kai hari, wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne kuma sun halaka dakaru da dama.

Blabrine na da nisan kilomita 20 daga yankin arewa maso yamma na garin Diffa a yankin kudu maso gabas din tafkin Chadi, inda iyakokin Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya suka hadu.

Diffa gari ne da ke da a kalla mutum 200,000 mai kusanci da iyakar Najeriya. Gari ne da ya saba samun hare-hare sakamakon zaman mayakan Boko Haram.

Garin ya bai wa a kalla 'yan gudun hijira 300,000 daga Najeriya masauki, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana.

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata, an kashe dakaru 13 na kasar Nijar a Blabrine, kamar yadda ma'aikatar tsaro ta bayyana.

'Yan ta'adda sun kai wa dakarun sojan Niger hari, sun halaka wasu

'Yan ta'adda sun kai wa dakarun sojan Niger hari, sun halaka wasu. Hoto daga HumAngle
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

An yi ta kai ruwa rana tsakanin mayakan Boko Haram da dakarun da ke yankin tun daga farkon watan Mayun nan.

A ranar 13 ga watan Mayun 2020, Niamey ta bayyana cewa an halaka mayakan Boko Haram 75 a yankin kudu maso gabas na Nijar da kuma tsallaken iyakar Najeriya.

A ranar 3 ga watan Mayun 2020, ISWAP ta saki wani bidiyo da ke nuna mayaka dauke da makamai sun tsinkayi sansanin sojoji inda suka fara musayar wuta da miyagun makamai.

Mayakan ta'addancin sun sake kai wani harin a wannan yankin a ranar Asabar.

Mayakan Boko Haram sun halaka sama da rayuka 36,000 a yankin arewa maso gabas din kasar nan tun bayan da ta fara bullowa Najeriya a 2019. A kalla mutum miliyan biyu ne suka bar gidajensu.

Amma tuni kasashen da ke yankin tafkin Chadin suka kafa wata kungiyar jami'an tsaro ta hadin guiwa don bada tsaro tare da dakile ayyukan 'yan ta'addan a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel