Kiristocin Arewa Sun Tsoma Baki kan Kisan da Aka Yi wa Malamar Islamiyya a Kaduna

Kiristocin Arewa Sun Tsoma Baki kan Kisan da Aka Yi wa Malamar Islamiyya a Kaduna

  • Shugabannin Kiristoci a Arewacin Najeriya sun yi alhini da ta'aziyya ga iyalan Malama Ummulkhairi Usman Aliyu
  • Kiristocin sun kuma yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa malamar Islamiyan a Maraban Jos, jihar Kaduna
  • Sun buƙaci gwamnati ta kamo tare da hukunta duk masu hannu a wannan mummunan kisa da aka yi wa malamar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Shugabannin Kiristocin Arewacin Najeriya sun kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu, matar aka kashe a Marabar Jos ta jihar Kaduna.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar kiristocin Arewa (NCA), Fasto Joseph John Hayab, ta kai ziyara zuwa gidan marigayiyar domin jajanta wa iyalanta tare da yin Allah wadai da kisan.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kungiyar NCA ta yi tir da kisan Malama

Kara karanta wannan

Martanin gwamnatin tarayya bayan kisan 'yan Najeriya 2 a Afirka ta Kudu

Leadership ta ce da yake jawabi, Hayab ya ce dole ne 'yan Najeriya su yi watsi da al'adar ɗaukar doka a hannu, yana mai jaddada cewa duk wanda ake zargi da wani laifi yana da haƙƙin samun adalci a gaban kotu.

Ya ce shugabannin Kiristocin sun ɗauki ziyarar a matsayin nauyi na addini da ɗabi'a, yana mai cewa addini ya kamata ya haɗa kan jama'a a lokacin baƙin ciki, ba ya raba su ba.

Hayab ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro su tabbatar da kamo tare da gurfanar da duk waɗanda suke da hannu a kisan.

Ya ce:

"Dole ne gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa irin wannan abin takaici bai sake faruwa ga wani ɗan Najeriya ba, ko Kirista ne, Musulmi ko mabiyin wani addini. Rayuwar ɗan Adam mai tsarki ce, kuma dole ne adalci ya rinjayi kisan gilla."

Kiristocin Arewa sun jajantawa mijinta

A yayin ziyarar, tawagar ta kuma yi magana ta wayar tarho da mijin marigayiyar, Malam Aliyu Mohammed, wanda ke ci gaba da karɓar magani a asibiti, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Hayab ya yaba da yadda Malam Aliyu ya yi haƙuri da nuna dattako duk da irin babban rashi da ya same shi, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Kara karanta wannan

Murkushe ƴan adawa da abu 3 da ƴan Najeriya ke fargaba game da ƴansandan jihohi

Mijin Ummulkhairi.
Malam Aliyu, mijin malamar Islamiyya da a kashe a Kaduna, tare da wasu yan uwansa Hoto: Usman Kabir Ahmad
Source: Facebook

Mijin Ummulkhairi ya roƙi a yi adalci

Da yake magana ta wayar tarho, Aliyu ya bayyana matuƙar godiyarsa ga shugabannin Kiristocin bisa ziyarar da suka kai wa iyalansa a wannan mawuyacin lokaci.

Ya ce duk da rashin lafiyar da ta hana shi karɓar baƙi kai tsaye, ziyarar da addu'o'insu sun ƙarfafa masa gwiwa tare da ba iyalansa kwanciyar hankali.

Ya kuma roƙi gwamnati ta tabbatar da cewa an yi wa marigayiyar adalci, yana mai nuna damuwa kan makomar 'ya'yan da ta bari.

An kama mutane fiye da 100

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa babu wanda zai tsallake hukunci har sai an tabbatar da adalci ga marigayiya Ummulkhairi Aliyu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa zuwa yanzu, jami'an yan sanda sun kama sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a lamarin.

A cewarsa, tuni aka gurfanar da mutum 41 daga cikinsu a gaban kotu kan zargin kisan kai, yayin da wasu 41 ke ci gaba da fuskantar bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262