Ba Dadi: Yadda Hare Haren Rasa Suka Kashe Daliba 'Yar Najeriya a Ukraine
- Wata daliba "yar Najeriya ta gamu da ajalinta sakamakon hare-haren da dakarun Rasha suka kaddamar a kasar Ukraine
- Matashiyar dalibar dai mai shekaru 23 ta rasa ranta ne bayan ta kammala karatun likitanci a wata jami'a da ke birnin Kharkiv
- Hare-haren dai sun ritsa da ita da wata kawarta ne ana sauran kwana daya su karbi takardar shaidar kammala karatunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Kharkiv, Ukraine - Nnani Adaobi Marian, wata ‘yar Najeriya mai shekaru 23 da ta kammala karatun aikin likita a Jami'ar Likitanci ta Kasa ta Kharkiv a Ukraine ta rasu.
Marigayiyar ta rasu ne bayan ta samu munanan raunuka sakamakon hare-haren Rasha a birnin Kharkiv na kasar Ukraine, kwanaki kalilan kafin taron yaye dalibai na kammala karatunta.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'ar ta fitar a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Makiyaya sun cinnawa dakin kwanan dalibai dauke da mutum 80 wuta? Yan sanda sun yi bayani
Hare-haren Rasha sun kashe 'yan Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa dakarun Rasha sun jefa bama-bamai ta sama a gundumar Kholodnohirskyi da ke Kharkiv a ranar 29 ga Yunin 2026, inda suka kashe mutane 14 a fadin yankunan Dnipropetrovsk, Zaporizhzhia, da Kharkiv, sannan suka jikkata wasu mutane 98.
Sanarwar ta bayyana cewa Marian ta samu munanan raunuka a harin, kuma daga baya ta rasu duk da kokarin da likitoci a Kharkiv da kasar Jamus suka yi na ceto rayuwarta.
“Sakamakon harin makamai na makiya, Nnani Adaobi Marian ta samu raunuka masu tsanani. Likitoci sun fafata domin ceto rayuwarta har zuwa lokacin karshe: da farko a Kharkiv, sannan daga baya a Jamus."
"Kowa ya nuna juyayi, ya taimaka, kuma ya yi fatan samun saukinta, amma, abin takaici, duk da dukkan kokarin likitocin, ba su iya ceto ta ba,” in ji jami'ar.
An bayyana dalibar a matsayin mai hazaka
Jami'ar ta bayyana cewa Marian ta yi rajista a makarantar ne a shekarar 2020, kuma ta nuna kanta a matsayin daliba mai hazaka, mai daukar nauyi, da kuma kwazo, wadda a kodayaushe take samun sakamako mai girma a karatunta.

Kara karanta wannan
Matakin Gwamna Abba ya ɗaga darajar Kano, ta hau matsayi na 1 a jerin jihohin ƙasashe 15
Makarantar ta kara da cewa ta jajirce sosai wajen ci gaban kwarewarta ta hanyar gudanar da horon aiki, ciki har da a Jami'ar Cambridge a shekarar 2024 da Jami'ar Biruni a shekarar 2025, inda ta inganta kwarewarta ta fannin likitanci tare da shiga cikin binciken kimiyya.
Yadda hare-haren suka ritsa da dalibar
An bayyana cewa Marian tana tafiya ne tare da kawarta, Fatima Huseynova, domin yin hotunan taron yaye dalibai a lokacin da harin ya auku.
Su biyun sun kasance wadanda ya kamata su karbi shaidar digirinsu na aikin likita a washegarin ranar da aka kawo harin.

Source: Twitter
An kashe Fatima a harin, yayin da Marian kuma ta samu raunuka masu tsanani da suka jefa rayuwarta cikin hadari, inda aka kai ta asibiti domin duba lafiyarta.
An ba da rahoton cewa daya daga cikin bama-baman ya fashe ne a kan wata hanya a gundumar Kholodnohirskyi da ke Kharkiv, lamarin da ya jikkata wasu mutane 12.
Dan Najeriya ya rasa ransa a yaki da Ukraine
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomi a kasar Ukraine sun bayyana mutuwar wani ɗan Najeriya mai suna Ayebusiwa Olabode Victor.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana zargin marigayin yana yaƙi tare da dakarun Rasha a yaƙin Ukraine domin taimaka mata.
Kisan na dan Najeriyan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna.
Asali: Legit.ng