'Yan Daban Siyasa Sun Hallaka Malamin Islamiyya a Bauchi

'Yan Daban Siyasa Sun Hallaka Malamin Islamiyya a Bauchi

  • Wasu mutane da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun yi aika-aikar kashe wani malamin Islamiyya a jihar Bauchi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan daban sun hallaka marigayin ne bayan ya yi masu magana kan shirinsu na sanya allon talla na wani dan siyasa
  • An bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ba ya wasa da neman na kansa domin ciyar da iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Wadansu mutane da ake zargin 'yan yan daba ne na siyasa, sun hallaka wani malamin Islamiyya, Ustaz Ridwan (Rilwanu) Dauda, a jihar Bauchi.

'Yan daban sun hallaka mutumin mazaunin unguwar Karofin-Madaki, ta hanyar caka masa wuka har lahira a kusa da na'urar canjin wuta ta JEDCO da ke cikin kwaryar birnin Bauchi.

An kashe malamin Islamiyya a Bauchi
Marigayi Ridwan da 'yan daba suka kashe a Bauchi Hoto: Bukhari Muazu Abubakar
Source: Facebook

Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa lamarin mai ban takaici ya faru ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026 biyo bayan wata zafafan muhawara da aka yi da yan daban game da manna hoton wani dan siyasa a jikin ginin.

Kara karanta wannan

"Babu sulhu": Gwamna Dauda ya fadi shirinsa kan kawo karshen 'yan bindiga

Yadda aka kashe malamin Islamiyya

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa marigayi Ridwan ya shaida wa mutumin cewa kada ya manna hoton a jikin bangon ginin nasu, amma mutumin ya ki, kuma ya nace a kan sai ya manna hoton.

An kuma kara samun labarin cewa dan daban na siyasar ya kira abokinsa, wanda ya zo wurin kuma ya ci gaba da manna hoton, lamarin da ya yi sanadiyyar barkewar zazzafar muhawara a tsakaninsu.

Mazaunin yankin ya ce a cikin wannan hali ne daya daga cikin yan daban ya zaro wata wuka mai kaifi ya daba wa marigayi Ridwan a kirji, sannan ya tsere.

A cewarsa, mazauna yankin sun rugo da gudu, suka kwashe marigayi Ridwan, kuma suka nufi asibiti da shi da sauri, amma kafin su karasa a kan hanya, ya cika.

An bayyana halayen marigayin

Wani mazaunin yankin daban ya bayyana Ustaz Rilwanu a matsayin mutumin kirki, mai natsuwa, kuma malamin makarantar Islamiyya mai kyakkyawan asali, wanda yake da kwazo da himma wajen neman abin da zai kula da iyalinsa.

Kara karanta wannan

Makiyaya sun cinnawa dakin kwanan dalibai dauke da mutum 80 wuta? Yan sanda sun yi bayani

Hakazalika, wani mazaunin yankin daban, Bukhari Mu’azu Abubakar, ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin faruwar lamarin mai ban takaici.

A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, Bukhari Mu’azu Abubakar ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin bisa mutuwarsa.

'Yan daba sun kashe malamin Islamiyya
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bukaci a dauki mataki

Ya kuma yi kira ga manya da shugabannin al'umma na yankin da su dauki matakan kariya domin kauce wa faruwar hakan a nan gaba.

Ya nuna alhininsa cewa marigayi Malam Rilwanu Dauda ya bar mace guda da yara biyar, inda ya nemi a yi adalci ga iyalan sannan kuma a dauki matakan gaggawa na taimaka wa iyalan a kan yadda za su ci gaba da rayuwa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, domin kuwa kakakinta, SP Nafiu Habib, bai amsa sakon da aka tura masa ta lambarsa ta WhatsApp ba game da wannan batu.

'Yan daba sun kashe dan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami'in dan sanda ya rasa ransa sakamakon fadan 'yan daba a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: Babban likita ya rasu mintuna 15 bayan ya zo duba marasa lafiya a Kano

Jami'in dam sandan ya rasu ne lokacin wani fada da aka yi tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba masu adawa da juna a Kano, saura watanni kaɗan ya yi ritaya.

An kashe shi ne tare da wasu mutane huɗu a lokacin fadan da ya faru a yankin Hotoro da ke karamar hukumar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng