A Yi Hattara: Katsina, Sokoto da Wasu Jihohi 25 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

A Yi Hattara: Katsina, Sokoto da Wasu Jihohi 25 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

  • Hukumar NiMet ta yi gargadin cewa jihohi 27 na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin 1 zuwa 10 ga Yulin 2026 sakamakon mamakon ruwan sama
  • Hukumar ta ce kasa ta riga ta koshi da ruwa bayan mamakon daminar Yuni, lamarin da zai iya haddasa ambaliya a birane da yankunan kwari
  • NiMet ta bukaci jama'a su guji shiga ruwan da ke tafiya, su tsaftace magudanan ruwa, sannan hukumomin agaji su kara shirin tunkarar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa jihohi 27 na kasar nan na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin ranar 1 zuwa 10 ga watan Yulin 2026.

Hukumar ta bayyana cewa ana sa ran mamakon ruwan sama zai ci gaba da sauka a wannan lokaci, yayin da ake kara nutsawa a cikin daminar a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

An saki bidiyon bama baman da Putin ya harba babban birnin Ukraine

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 27 na Najeriya
Wasu garuruwa da suka nutse a cikin ruwa bayan ambaliya a Borno. Hoto: Audu Marte via Getty Images
Source: Getty Images

Jihohi 27 za su fuskanci ambaliya

A cikin sanarwar da ta fitar, NiMet ta ce yawan ruwan saman da aka samu a watan Yuni ya sa kasa ta riga ta koshi da ruwa, wanda hakan ya rage karfinta na tsotse karin ruwan sama, in ji rahoton Punch.

Hukumar ta ce hakan na kara yiwuwar aukuwar ambaliyar cikin kankanin lokaci, musamman a yankunan kwari, birane, wuraren bakin teku da kuma wuraren da ba su da ingantattun magudanan ruwa.

NiMet ta ce jihohin da ke cikin hadarin sun hada da:

  1. Taraba
  2. Sokoto
  3. Borno
  4. Zamfara
  5. Kebbi
  6. Katsina
  7. Kaduna
  8. Nasarawa
  9. Plateau
  10. Adamawa
  11. Kwara
  12. Kogi
  13. Oyo
  14. Ogun
  15. Legas
  16. Osun
  17. Ekiti
  18. Delta
  19. Edo
  20. Abia
  21. Imo
  22. Anambra
  23. Enugu
  24. Akwa Ibom
  25. Cross River
  26. Rivers
  27. Bayelsa

Matsalolin da ake sa ran za su biyo baya

Hukumar ta yi gargadin cewa mamakon ruwan saman na iya haddasa cunkoson ababen hawa, rufe hanyoyi da kawo tsaiko ga harkokin sufuri.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Ta kuma ce ana iya samun katsewar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa a wasu wurare, yayin da rashin gani sosai a lokacin ruwan sama zai iya jefa direbobi da jiragen sama cikin hadari.

Bugu da kari, NiMet ta ce ambaliyar na iya lalata gonaki, haddasa asarar amfanin gona tare da lalata hanyoyi, gadoji, magudanan ruwa da sauran kayayyakin more rayuwa.

Hukumar NiMet ta ba da shawarwari

NiMet ta gargadi 'yan Najeriya da su dauki matakai yayin da ake tunkarar ambaliya a jihohi 27
Shugaban hukumar NiMet tare da wasu ma'aikata suna girka na'urar hasashen yanayi. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito hukumar ta bukaci 'yan Najeriya su rika bibiyar hasashen yanayi da gargadin ambaliya, tare da tabbatar da tsaftace magudanan ruwa domin saukaka kwararar ruwa.

Haka kuma ta shawarci jama'a da su guji tafiya ko tuki cikin ruwan da ke gudu, su tabbatar sun tsare kayayyakin da ke waje, sannan su karfafa gine-ginen da ka iya fuskantar hadari.

NiMet ta kuma bukaci hukumomin bayar da agajin gaggawa kamar NEMA, SEMA da shugabannin al'umma su kara shirye-shiryen tunkarar yiwuwar ambaliyar domin rage asarar rayuka da dukiyoyi.

2026: Jihohi za su fuskanci ambaliya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ministan albarkatun ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta shiga batun ma'aikatar bogi, ta aika sako ga gwamnatin Tinubu

Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.

Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com