Siyasar Kaduna: Bayan El Rufa'i, Ashiru Kudan Ya Yi Rubdugu ga Uba Sani

Siyasar Kaduna: Bayan El Rufa'i, Ashiru Kudan Ya Yi Rubdugu ga Uba Sani

  • Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kaduna, Isa Ashiru Kudan, ya caccaki gwamnatin jihar bisa zargin nuna son kai
  • Ya zargi gwamnatin jihar da amfana da goyon bayan gwamnatin tarayya ba tare da kulawa da walwalar al’ummar Kaduna ba
  • Ashiru Kudan ya yi ishara ga al’ummar jihar Kaduna da su farka su tsaya tsayin daka wajen kare muradunsu a harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Isa Mohammed Ashiru Kudan, ya fito fili yana sukar gwamnatin jihar ƙarƙashin Uba Sani.

Ashiru Kudan ya zargi gwamnatin da rashin adalci wajen gudanar da al’amura da kuma amfani da tallafin kudi daga gwamnatin tarayya ba tare da amfani da shi wajen sauƙaƙa wa talakawa ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya fara gyara hanyar Saminaka da ta hada jihohin Arewa

Uba Sani
An zargi gwamnan Kaduna da nuna wariya. Hoto: Isa Ashiru Kudan|Uba Sani
Asali: Twitter

Legit ta gano maganganun da Isa Ashiru Kudan ya yi ne a cikin ani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da ya fitar ga al’ummar jihar Kaduna, Ashiru ya bayyana damuwarsa kan zargin yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da mulki cikin son kai da nuna fifiko ga wasu.

Zargin rashin adalci wajen rabon tallafi

Ashiru Kudan ya bayyana cewa akwai rashin daidaito a yadda gwamnatin Kaduna ke amfani da tallafin kudi da take samu daga gwamnatin tarayya.

"Tsawon watanni, mun shaida yadda gwamnan Kaduna ke aikata abin kunya kala kala, tare da furuci da daukar matakai da ke nuna rashin tabbas da son zuciya."
"Yanzu komai ya bayyana. Jihar na samun tallafin kudi daga gwamnati amma al’ummar jihar na ci gaba da fama da ƙuncin rayuwa."
"Dole ne mu tambayi kanmu: Ina muka nufa a wannan yanayin?"

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

Ashiru Kudan ya yi zargin cewa Uba Sani na nuna dabarar siyasa domin nuna fifiko ga wasu mutane kalilan, yayin da yawancin jama’a ke cikin talauci.

Kudan ya ce ana wahalar rayuwa a Kaduna

Isa Ashiru ya ce al’ummar jihar Kaduna na da haƙƙin sanin gaskiya game da yadda ake tafiyar da kudaden da suka kamata su amfani kowa da kowa.

"Gwamnatin nan ta yi alkawarin kawo sauki, amma abin da muke gani shi ne nuna son kai, sabon salon yaudara da ƙuncin rayuwa ga mafi yawan jama’a.
"Amma ku sani—tarihi ba zai manta ba. Mutanen Kaduna za su yi hukunci a lokacin da ya dace,"

- Isa Ashiru Kudan

'Mulki ba ya tabbata' - Ashiru Kudan

Ashiru Kudan ya kuma bayyana cewa ikon mulki ba abu ne na dindindin ba, yana mai gargadin masu mulki da su tuna cewa za su sauka a madafun iko kuma za a tuna ayyukan da suka yi.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kaduna: El Rufa'i ya nuna yatsa ga Uba Sani kan Tinubu

"Ga wadanda ke tunanin su ne masu fada a ji a yau a jihar Kaduna, ku sani cewa mulki ba ya dawwama,"

- Isa Ashiru Kudan

El-Rufa'i ya yi martani ga Uba Sani

A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i ya yi martani mai zafi ga gwamna Uba Sani.

Legit ta rahoto cewa El-Rufa'i ya yi magana ne bayan wata hira da Uba Sani ya yi inda ya ce har yanzu yana da alaka mai kyau da tsohon gwamnan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng