Elon Musk Ya Taba Trump, Ya Ce Afirka Ta Tsira da Amurka Ta Bar ba Ta Agaji

Elon Musk Ya Taba Trump, Ya Ce Afirka Ta Tsira da Amurka Ta Bar ba Ta Agaji

  • Attajiri Elon Musk ya yi magana game da ta rage tallafin USAID da Amurka ke bayar wa a Afirka, yana cewa hakan ya rage rikice-rikice a nahiyar
  • kwaararrun masana lafiya da ƙungiyoyin agaji sun gargadi cewa rage tallafin na iya jawo mutuwar fiye da mutum miliyan 14 a duniya nan da 2030
  • Musk ya dage cewa an rage tallafin ne domin dakile almubazzaranci da cin hanci, yana zargin wasu shirye-shiryen USAID

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya yi iƙirarin cewa adadin mutuwar mutane a faɗin Afirka ya ragu sosai.

Elon Musk ya ce hakan ya faru ne bayan Amurka ta rage tallafin ƙasashen waje wanda a baya take bayar wa a Nahiyar.

Musk ya ce Afirka ta samu sauki bayan yanke agajin Amurka
Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk da Shugaba Donald Trump. Hoto: @RealDonaldTrump, @elonmusk.
Source: Getty Images

Musk ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake mayar da martani kan sukar Ma'aikatar Inganta Ingancin Gwamnati (DOGE), cewar rahoton Forbes.

Kara karanta wannan

Zafi ya shiga Turai yana ta kashe mutane a Faransa da sauran kasashe

Musk ya magantu kan tallafin Amurka a Afirka

Musk ya ce dakatar da wasu shirye-shiryen agaji ya taimaka wajen rage rashin zaman lafiya a nahiyar.

Ya goyi bayan matakan rage kashe kuɗi da suka haifar da gagarumin rage kasafin Hukumar Agajin Ƙasashen Waje ta Amurka (USAID).

Sai dai Musk ya nuna bayanan mace-mace daga wasu ƙasashen Afirka, ya ce alkaluman ba su nuna wata ƙaruwa mai yawa ta mace-mace ba bayan rage tallafin.

Ya rubuta cewa:

"Mutuwar mutane a Afirka ta ragu bayan an rage tallafin USAID, domin ba sa iya tallafa wa juyin juya halin tashin hankali domin kafa gwamnatocin masu ra'ayin hagu."

A cewar ƙungiyar Refugees International, tallafin jin ƙai na Amurka ya ragu daga dala biliyan 14 a shekarar 2024 zuwa dala biliyan 3.7 a shekarar 2025. Ƙungiyar ta ce rufe ayyukan USAID ya zama babban misali na raguwar agajin jin ƙai a duniya.

Elon Musk ya caccaki tallafin hukumar USAID a Afirka
Shugaban kamfanin TESLA, Elon Musk. Hoto: @elonmusk.
Source: AFP

Yawan kudaden USAID da aka kashe ya ragu

Haka kuma, 'Center for Global Development' ta bayyana cewa kuɗaɗen da hukumar USAID ta kashe sun ragu da kusan kashi 58 cikin ɗari a shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kano: An gano abin da ya jawo mummunan arangama tsakanin manoma da makiyaya

Duk da wannan raguwar, masana harkokin lafiya da ƙungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa rage tallafin na iya haifar da mummunan sakamako ga jin daɗin al'umma a sassa daban-daban na duniya, cewar Tribune.

Jadawalin ya nuna cewa yawan mace-macen da aka lura da su ya ci gaba da kasancewa kusa da sifili, kuma ya kasance ƙasa da hasashen da aka yi kafin rage tallafin.

Musk ya ci gaba da kare matakin rage tallafin, yana cewa manufarsa ita ce rage almubazzaranci, cin hanci da kuma amfani da kuɗin masu biyan haraji wajen manufofin siyasa maimakon ayyukan jin ƙai.

Ya kuma yi zargin cewa wasu ayyukan USAID a wasu sassan Afirka sun ƙarfafa juyin juya hali domin kafa gwamnatocin masu ra'ayin hagu. A cewarsa, kawo ƙarshen irin wannan tallafi ya rage tushen rikice-rikice.

Musk ya fadi abin da ya fi karfin kudi

Mun ba ku labarin cewa Elon Musk, attajirin da ya fi kowa kudi a duniya ya haddasa muharawa a kafafen sada zumunta kan farin cikin 'dan adam a rayuwa.

Hamshakin attajirin ya gamsu da hikimar masu zance da ke cewa kudi ba su iya sayen farin ciki, inda ya ce masu wannan magana sun fahimci rayuwa.

Wannan kalamai sun haddasa shakku daga mabiyan attajirin, wasu na ganin maganar haka take, wasu kuma na cewa kudi na samar da damarmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.