Wata Sabuwa: Majalisar Dattawa na Son INEC Ta Hana Wasu 'Yan Takara Tsayawa Zabe a 2027
- Majalisar Dattawa ta buƙaci INEC ta hana duk ɗan takarar da magoya bayansa suka shiga rikicin zaɓe tsayawa takara
- Sanatoci sun buƙaci jami’an tsaro su binciki rahotannin hare-hare a Abuja, Edo, Delta da Sokoto tare da gano waɗanda suka aikata su da masu ɗaukar nauyinsu
- Majalisar ta kuma buƙaci gwamnoni su daina hana jam’iyyun adawa amfani da otal-otal da filayen wasa na gwamnati wajen gudanar da harkokin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta hana duk wani ɗan takarar siyasa tsayawa takara idan aka samu magoya bayansa suna tunzura mutane ko shiga ayyukan tashin hankali a lokacin zaɓe.
Majalisar ta ce ya kamata a aiwatar da wannan mataki ba tare da la’akari da jam’iyyar da ɗan takarar yake wakilta ba, bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma hukuncin kotu da ya tabbatar da aikata laifin.

Source: Facebook
Majalisar ta buƙaci INEC ta aiwatar da dokar
Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana cewa INEC na da ikon hana ɗan takara tsayawa takara idan aka kama shi ko magoya bayansa suna tunzura mutane zuwa tashin hankali, cewar rahoton tashar Channels tv.
"Duk ɗan takara ko magoya bayansa da aka kama suna tunzura mutane zuwa rikici, INEC na da ikon hana shi tsayawa takara.
“Ya kamata mu jawo hankalin INEC kan tanadin Dokar Zaɓe ta 2026. Ko da wace jam’iyya ɗan takarar yake ciki, ya kamata a hana shi tsayawa takara nan take idan an tabbatar da laifin. An tanadi waɗannan matakai a cikin dokar ta 2026, kuma suna buƙatar aiwatarwa da ƙarfi.” In ji shi.
Shugaban majalisar ya buƙaci hukumar zaɓen ta tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden dokar da suka shafi hukunta masu hannu a rikicin zaɓe.
Ya kuma jaddada muhimmancin tsaurara matakan aiwatar da dokar gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin
Sanatoci sun nemi a binciki hare-haren siyasa
Wannan matsaya ta biyo bayan wani ƙuduri da Sanata Abdul Ningi ya gabatar kan buƙatar gaggauta dakile ƙaruwar rikici, rashin haƙuri da hare-hare kan shugabannin siyasa da magoya bayansu a Najeriya.
Ƙudurin ya samo asali ne daga rahotannin hare-haren baya-bayan nan kan ’yan siyasa, ciki har da lamarin da ya shafi Shugaba Bola Tinubu a wani masallaci ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026.
A yayin muhawara mai zafi kan ƙudurin, sanatocin sun buƙaci hukumomin tsaro su binciki rahotannin hare-hare a jihohi huɗu, wato Abuja, Edo, Delta da Sokoto.
Sun kuma nemi jami’an tsaro su gano waɗanda suka aikata hare-haren da kuma mutanen da suka ɗauki nauyinsu, tare da tabbatar da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
An nemi ƙarfafa tsaron ’yan siyasa
Sanatocin sun nuna damuwa kan yadda zaman siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a ƙasar.
Saboda haka, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta umarci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro su ƙarfafa tsaron shugabannin siyasa, ’yan takara, magoya baya da wuraren tarukan siyasa a faɗin ƙasar.
Sun kuma buƙaci samar da ingantattun hanyoyin gano barazanar hare-hare tun da wuri da kuma ɗaukar matakin gaggawa domin hana aukuwarsu kafin babban zaɓen 2027.
An gargadi gwamnonin jihohi
Majalisar Dattawa ta kuma buƙaci gwamnonin jihohi su daina hana jam’iyyun adawa amfani da wuraren da gwamnati ke kula da su, ciki har da otal-otal da filayen wasa, domin gudanar da harkokin siyasa.
Sanatocin sun ce wajibi ne a tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa suna samun dama iri ɗaya wajen gudanar da ayyukansu.
Sun yi gargaɗin cewa hana jam’iyyun adawa gudanar da harkokinsu na iya ƙara rura wutar rashin haƙuri a siyasa da kuma haddasa rikice-rikicen da za a iya kauce musu.

Source: Facebook
Rikicin zabe: An bukaci INEC ta dauki mataki
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar da ke fafutukar kare haƙƙin jama'a da tabbatar da riƙon amana a Najeriya (SERAP) ta ba hukumar INEC wa'adi kan rikici a kamfen 2027.
SERAP ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gaggauta ɗaukar mataki kan rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a sassan ƙasar nan.
Asali: Legit.ng

