Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa

Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa

- A ranar Talata, UNFPA ta ce kashi 50 bisa 100 na masu HIV karuwai ne da 'yan luwadi

- A cewarta, dole ne duk mai kanjamau ya kiyaye kansa daga COVID-19 don za ta iya ajalinsa

- Darektan UNFPA, Dr Natalia Kanem ce ta shaida hakan a Abuja, a ranar kanjamau ta duniya

A ranar Talata, UNFPA tace kashi 50 bisa 100 cikin wadanda basu dade da samun kanjamau ba, karuwai ne da 'yan luwadi.

Sai dai ta yi takaicin sanar da cewa kaso kadan ne daga kudaden da aka ware don shawo kan HIV za a sadaukar garesu, jaridar Vanguard ta tabbatar.

UNFPA ta bayyana hakan a wata takarda wacce darektan ta, Dr Natalia Kanem ta gabatar a Abuja ta zagayowar ranar kanjamau ta duniya ta shekarar 2020, wacce tayi wa take da, "Kawo karshen cutar HIV/AIDS: Janyo masu cutar a jiki, da kwantar musu da hankali."

KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Duk malamin da bai yi huduba a kan tsaro ba munafuki ne, Malam Maraya

Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa
Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata

UN ta bayyana yadda masu HIV za su fi saurin kamuwa da cutar COVID-19 kuma ta illata su.

Kanem ta ce mafi yawan wadanda suke samun cutar HIV a fadin duniya, karuwai ne da kuma maza 'yan luwadi. Suna samun cutar ne sakamakon yin jima'i da mutane daban-daban.

"Alamu sun nuna cewa babban hatsarin da masu HIV za su fuskanta shine idan suka kamu da COVID-19 don hakan zai iya sanadiyyar mutuwarsu cikin kankanin lokaci."

A cewarta, matsawar ana son kawo karshen HIV, wajibi ne a dinga janyo masu cutar a jiki.

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Olusegun ya bayyana irin bakar wahalar da ya fuskanta a soyayya lokacin yana daukar albashin N20,000.

Saurayin ya wallafa labarin abinda ya faru tsakanin shi da budurwarsa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarsa, sun dan fita yawon shakatawa da shi da budurwarsa, ya siya wa kansa ruwa, ita kuma budurwar ta bukaci abincin N4500.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng