Lokaci Ya Yi: Tsohon Babban Kwamishina a Gombe Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An yi rashi a jihar Gombe na tsohon kwamishinan da ya yi aiki a gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya
- Tsohon kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Gombe, Hon. Ibrahim El-Hassan Kwami, ya yi bankwana da duniya bayan jinyar rashin lafiya
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike da sakon ta'aziyyarsa bisa rasuwar marigayin wanda suka taba yin aiki tare a gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Gombe, Hon. Ibrahim El-Hassan Kwami ya rigamu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026 a Gombe bayan ya yi fama da gajeruwar jinyar rashin lafiya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an binne gawarsa bayan an yi sallar jana'iza, wadda aka gudanar a Masallacin Juma'a na Fadar Sarkin Gombe.
Ya taba aiki a gwamnati
Marigayin ya yi aiki a matsayin kwamishinan yada labarai da al'adu, daga watan Nuwamba na shekarar 2019 zuwa watan Maris na shekarar 2021, lokacin mulkin farko na Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Marigayi Kwami, wanda ya yi aiki da hukumar haraji ta kasa (NRS), an cire shi ne yayin wani dan karamin garambawul da aka yi wa majalisar zartarwa a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2021.
Gwamna Inuwa ya yi ta'aziyya
A halin da ake ciki kuma, Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna alhini dangane da rasuwar tsohon kwamishinan.
Ya tuno da irin gagarumar gudunmawar da marigayi Ibrahim Kwami ya bayar wajen ci gaban jihar lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan yada labarai, inda ya bayyana cewa ya nuna kwazo na musamman da kuma matukar rikon amana wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya
Ya yaba da ayyukansa
Gwamnan ya bayyana kyakkyawan aikin da marigayin ya yi a NRS, "inda ya shahara a matsayin kwararre a fannin kudi, kuma jajirtaccen ma'aikacin gwamnati wanda dimbin gogewarsa ta amfani jihar da ma kasa baki daya."
Ya bayyana mutuwar marigayi Ibrahim El-Hassan Kwami a matsayin babban rashi ba ga iyalansa da al'ummar Kwami kadai ba, har ma ga jihar da ma Najeriya baki daya.

Source: Facebook
Gwamna Inuwa Yahaya ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, da shugabanni da ma'aikatan NRS, da al'ummar Kwami, da kuma abokansa da sauran abokan arziki.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki (SWT) da ya yafe wa marigayin kura-kuransa, ya ba shi masauki a Aljanna Firdaus, kuma ya ba iyalansa juriya na jure wannan babban rashi.
Babban likita ya rasu a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani kwararren likitan da ke aiki a Jihar Kano ya rasu bayan ya fadi jim kadan bayan ya isa Asibitin Arewa Surgery da ke Hotoro.

Kara karanta wannan
Mutanen da 'yan bindiga suka sace a wurin Ibada sun dawo gida, mutum 1 ya mutu a Ekiti
Lamarin ya faru ne bayan an bukaci marigayin, wanda aka bayyana sunansa da Dokta Ibrahim, ya maye gurbin wani likitan da ya kasa halartar aikinsa na yamma.
An garzaya da shi sashen kula da marasa lafiya na gaggawa, inda wasu manyan likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarsa, amma cikin mintuna 15 aka tabbatar da rasuwarsa.
Asali: Legit.ng
