'Diyar Shugaban Kasa, Hanan Buhari, Ta Bude Gidauniyar Kanta Yau a Aso Villa

'Diyar Shugaban Kasa, Hanan Buhari, Ta Bude Gidauniyar Kanta Yau a Aso Villa

  • Hanan Buhari, daya daga cikin 'yayan shugaba Muhammadu Buhari ta yi Alla-wadai da yadda ake fyade a Najeriya
  • Hanan ta kaddamar da sabuwar gidauniyar kare hakkin yara da mata da ake cin zarafi a Najeriya
  • Hanan tana auren Muhammad Turad Sha'aban, 'dan tsohon dan takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna

Abuja - Diyar shugaban kasar Najeriya, Hanan Buhari, a ranar Juma'a ta yi Alla-wadai da yadda ba'a kai karan masu yiwa yan mata fyade a Najeriya.

Hanan Buhari ta bayyana hakan yau yayin kaddamar da sabon gidauniya da ta yiwa suna 'Hanan Buhari Foundation' a farfajiyar taron shugaban kasa dake Aso Villa, Abuja, rahoton Punch.

Hanan
'Diyar Shugaban Kasa, Hanan Buhari, Ta Bude Gidauniyar Kanta Yau a Aso Villa
Asali: Twitter

A jawabinta, Hanan Buhari ta jaddada cewa akwai bukatar magance matsalar fyade kuma a daina shiru idan abin ya faru.

A cewarta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A 2018, rahoton binciken hukumar yan sanda da ma'aikatar shari'a ya nuna cewa fyade da ake yiwa yan mata na kara yawa. "
"Duk da gwagwarmayar da ake yi, ana fyaden nan amma ba'a samun labari. Bisa rahoton hukumar hana fasa kwabrin mutane, kashi 32% na fyade kadai aka kai kara tsakanin 2019 da 2022."
"Wajibi ne a daina shiru. Musamman yanzu da mata suka fara samun karfin gwiwar magana kan cin zarafin da ake musu."

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Ministar harkokin mata, Pauline Tallen.

Ta bayyana cewa karkashin mulkinta, adadin jihohin Najeriyan da aka kafa dokar kare mutuncin yara tashi daga 12 zuwa 34.

Hanan Buhari ta samu 'karuwar da namiji

Zaku tuna cewa diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan tare da mijinta Muhammad Turad Sha’aban, sun samu karuwar da namiji a kasar Turkiyya.

Ma'auratan sun samu karuwar ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, 2022 a kasar Turkiyya, nahiyar Turai.

Mijin ta Muhammad Turad ya rubuta a shafin na Instagram cewa:

“Allah ya azurta ni da matata da haihuwar da namiji! Alhamdulillah.
“Mun saka masa suna Muhammad Zayd (Hibbu Rasulallah)."

Idan za ku tuna, Hanan ta auri sahibin nata ne a watan Satumban 2020, a wani gagarumin shagali da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel