Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure

Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure

- Wata daya bayan daurin aure, Hana da maigidan sun saki sabbin hotuna

- An daura musu aure a Masallacin fadar shugaban kasa ta Aso Villa

A daurin aurensu, wanda manyan mutane a fadin Najeriya suka halarta, Amaryar da Angon sun samu albarkan iyaye da manyan malamai.

Amma an yi cece-kuce kan yadda aka gudanar da daurin auren.

Yan Najeriya da dama sun caccaki iyalan shugaban kasa a kan karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) a wajen bikin Hanan Buhari, daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mutane da dama sun kuma yi wasti da take dokar bayar da tazara a tsakanin jama’a wanda hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayar don hana yaduwar cutar Coronavirus.

Bikin ya samu manyan jami’an gwamnati da yan siyasa. Hotuna da bidiyon bikin ciki harda wanda uwargidar shugaban kasar, Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram sun yi fice a karshen makon.

Turan 'da ne ga Mahmud Sani Sha'aban, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Zaria a majalisar wakilan tarayya daga Mayun 2003 zuwa 2007.

Hakazalika ya yi takaran kujeran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

Kalli hotunan:

Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure
Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure
Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

KU DUBA: An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure
Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan makonni biyu, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa

A wani labarin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli ya kai wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero ziyara ta musamman jiya, don kara dankon zumuntar da ke tsakanin masarautun guda biyu.

Ya ce ya kai ziyarar ne don kara dankon zumuncin da ya dade tsakanin masarautar Zazzau da ta Kano tun lokacin Sheikh Usman Fodio, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel