Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Farashin Mitar Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Farashin Mitar Wutar Lantarki

  • Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙarin farashin mitar wutar lantarki a duka fadin ƙasar nan
  • Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar da ke sanya ido kan wutar lantarki ta Najeriya (NERC)
  • Hakan a cewar sanarwar, zai taimakawa kamfanonin damar samun isassun kuɗaɗen da za su ci gaba da kula da mitocin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar, ta Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Najeriya (NERC), ta sanar da ƙarin farashin mitar wutar lantarki a duka fadin ƙasar nan.

Shugaban hukumar Sanusi Garba, da kwamishinan shari'a, bada lasisi da bin doka, Dafe Akpeneye ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An kara farashin mitar wutar lantarki
Gwamnatin Tarayya ta ƙara farashin mitar wutar lantarki. Hoto: Pulse
Asali: UGC

Sabon farashin mitar wutar lantarki

Sanarwar ta bayyana cewa mitar wutar da ake badawa a baya a kan naira 58,661.69, yanzu za ta koma naira 81,975.16, yayin da babbar wannan da ake badawa akan naira 109,684.36, yanzu za ta koma naira 143,836.10.

Kara karanta wannan

Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Ɓacewar Mutane 10,000 a Libya, Da Dama Sun Rasa Rayukansu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ci gaba da cewa ƙarin farashin ya zama dole ne domin tabbatar da adalci tsakanin kamfanonin da 'yan Najeriya masu amfani da mita.

Ta kuma ƙara da cewa hakan zai bai wa kamfanonin damar dawo da kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da mitar da kuma kula da ita.

Obasanjo ya musulunta batun ba da kwangilar wuta ta dala biliyan 6

A baya Legit Hausa ta yi rahoto kan martanin da tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi wa ɗaya daga cikin ministocinsa da ya yi iƙirarin cewa ya ba da kwangilar wuta ta dala biliyan shida.

Obasanjo ya buƙaci Olu Agunlayo da ya fito ya yi wa 'yan Najeriya bayanin yadda ya samu izinin bayar da kwangilar waɗannan maƙudan kuɗaɗe a lokacin da yake minista.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Najeriya Ta Ƙara Yin Babban Rashi

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Obasanjo ya ce babu wani ministan da ke da hurumin bayar da kwangilar da ta wuce ta miliyan 25 a lokacinsa.

Minista ya nemi 'yan Najeriya su daina zagin ma'aikatan wutar lantarki

A wani rahoto na daban da Legit Hausa ta yi a baya, ministan harkokin wutar lantarki Adebayo Adelabu, ya roƙi 'yan Najeriya su daina zagin ma'aikatan wutar lantarki.

Adelabu ya bayyana cewa ma'aikatar wutar a ƙarƙashin jagorancinsa za ta zo da tsare-tsaren da za su haɓɓaka wutar lantarki a Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng