Mutuwar Al-Baghdadi: Kungiyar ISIS ta yi sabon shugaba

Mutuwar Al-Baghdadi: Kungiyar ISIS ta yi sabon shugaba

Kungiyar ta'addanci ta 'Islamic State of Iraq and the Levant da aka fi sani da ISIL ko ISI ta tabbatar da mutuwar shugaban ta, Abu Bakr al-Baghdadi, ta kuma sanar da nada sabon shugaba da zai maye gurbinsa mai suna Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.

Sabon mai magana da yawun ISIS, Abu Hamza al-Qurayshi ne ya fitar da sanarwar cikin wata sakon murya da aka wallafa ta kafar watsa labarai na kungiyar mai suna Al Furqan.

Ya kuma tabbatar da mutuwar tsohon mai magana da yawun kungiyar, Abu al-Hassan al-Muhajir.

Channels TV ta ruwaito cewa wani sashi da cikin sakon murnar ya na cewa, "muna juyayin rashin ka ... shugaban masu imani", kamar yadda sabon mai magana da yawun kungiyar Abu Hamza al-Qurayshi ya fadi.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa a ranar Lahadi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa an kashe tsohon shugaban na ISIS, Abubakar Al-Baghdadi a wani harin da jami'an sojin Amurka suka kai masa a Arewa maso yammacin Siriya.

Trump ya sanar da duniya cewa sojojin sun kashe mayakan ISIS da dama kuma suna gab da damke Al-Baghdadi amma ya tayar da bam ya kashe kansa.

"Ya tayar da rigar bam, ya kashe kansa" a cewar Trump.

"Ya mutu bayan ya kai karshen rami in da ya ke kuka."

Shugaba Trump ya ce an kai harin ne tare da taimakon kasar Rasha, Siriya, Turkiyya da Iraqi.

An dade ana neman Abubakar Al-Baghdadi ruwa a jallo bayan kisan dubban mutane da kungiyar ta ISIS ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel