Tsaro: Gwamna Fintiri Ya ba Tsohon Sakataren Gwamnatin Marigayi Buhari Mukami
- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nada tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha mukami a jihar
- Gwamnatin Adamawa ta ce nadin ya nuna kudurinta na karfafa tsarin tsaro da tabbatar da wakilcin jihar
- Fintiri ya bayyana Boss Mustapha a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati wanda zai taimaka wajen cimma manufofin asusun da bunkasa hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya amince da nadin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, a matsayin wakilin jihar.
Zai wakilci Adamawa ne a kwamitin amintattu na Asusun Tsaron Arewacin Najeriya, wanda aka kafa domin tallafawa kokarin inganta tsaro a yankin.

Source: Facebook
Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar wanda Punch ta samu.
Musabbabin nba Boss Mustapha mukami a Adamawa
Sanarwar ta ce nadin ya nuna kudurin gwamnatin Adamawa na karfafa tsarin tsaro da tabbatar da wakilci a cibiyoyin yanke hukunci.
An bayyana cewa kungiyar gwamnonin Arewa ne ta kafa Asusun Tsaron Arewacin Najeriya domin taimaka wa hukumomin tsaro.
Asusun na da manufar tallafawa tattara bayanan sirri, samar da kayan aiki da kuma bunkasa hadin gwiwa tsakanin jihohin Arewa.
Haka kuma an kafa shi ne domin karfafa shirye-shiryen tsaro da suka samo asali daga al’ummomi a dukkan jihohi 19 na Arewa.
Da yake magana kan nadin, Fintiri ya bayyana Boss Mustapha a matsayin gogaggen jami’in gwamnati mai kwarewa da nagartaccen shugabanci.
Ya ce dimbin gogewa da matsayin da Mustapha ke da shi a kasa sun sa ya dace da wannan muhimmin mukami.

Source: Twitter
Gwamna Fintiri ya nuna damuwa kan matsalar tsaro
Gwamnan ya kuma nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya, musamman a yankin Arewa.
A cewarsa, yawaitar barnar ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da rikice-rikicen al’umma na bukatar sababbin matakan dakile su.
Fintiri ya ce yana da yakinin cewa Mustapha zai yi amfani da kwarewarsa wajen ciyar da manufofin asusun gaba, cewar TheCable.
Ya kara da cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar zai taimaka wajen karfafa hadin kai tsakanin jihohin Arewa kan harkokin tsaro.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Adamawa da sauran yankunan Arewa.
Sauya sheka: Fintiri ya gargadi hadimansa
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya gargadi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ba sa goyon bayan jam'iyyar APC.
Ya bukaci waɗanda ba su APC ko suka fito fili suka nuna biyayya ga wasu jam’iyyun siyasa da su yi murabus daga muƙamansu nan take ko ya kore su.
A cewar gwamnan, an bai wa waɗanda abin ya shafa wa’adin sa’o’i 48 su miƙa takardun murabus dinsu ga ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

