Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da sabbin jagororin majalisar a zaman yau Talata, 4 ga watan Yuli, 2023
  • Akpabio ya bayyana waɗanda suka samu nasarar zama shugaban masu rinjaye, marasa rinjaye, mai ladabtarwa da mataimakansu
  • Bamidele, Dave Umahi, da Sanata Ali Ndume na cikin sabbin jagororin da aka ji Akpabio ya ambaci sunayensu a zaman Sanatoci

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da waɗanda suka samu nasarar zama jagororin majalisar dattawa ta 10.

Channels tv ta tattaro cewa Sanata Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi sabbin shugabannin ne ta hanyar maslaha.

Sabbin jagororin majalisar dattawa ta 10.
Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa Hoto: channelstv
Asali: UGC

Jagororin bangaren masu rinjaye

Sabbin jagororin majalisar sun haɗa da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Dave Umahi daga Ebonyi a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sunayen Sabbin Jagororin Majalisar Wakilan Tarayya Ta 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya zama babban mai ladaftarwa na majalisa yayin da Sanata Lola Ashiru, ya samu nasarar zama mataimakinsa.

Sabbin jagororin majalisar dattawa daga ɓangaren marasa rinjaye

A ɗaya bangaren kuma Sanata Akpabio ya bayyana sabbin shugabanni daga ɓangaren marasa rinjaye.

Sun ƙunshi Sanata Simon Davou (Filato ta arewa – PDP) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye yayin da Oyewunmi Olarere (Osun ta yamma – PDP) ya zama mataimakinsa.

Sauran sun haɗa da Sanata Darlington Nwokeocha mai wakiltar jihar Abia ta tsakiya a inuwar LP a matsayin mai ladaftarwan marasa rinjaye da kuma Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya) a matsayin mataimakinsa.

Idan baku manta ba 'yan takarar da jam'iyyar APC ta marawa baya ne suka samu nasarar zama shugabannin majalisar tarayya ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Godswill Akpabio ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa yayin da Honorabul Tajudeen Abbas ya zama sabon kakakin majalisar wakilan tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Sani Yerima

A wani labarin na daban kuma bayam ganawa da shugaban kasa, Sanata Yerima ya ce shugaba Tinubu ya ɗora masa alhakin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta yi wa katutu a shiyyar Arewa maso Yamma yayin da 'yan bindigan jeji da masu garkuwa suka hana mutane rawar gaban hantsi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262