Yar'Adua Bayan Shekaru 11: Abubuwa 6 Game da Marigayi Tsohon Shugaban Najeriya

Yar'Adua Bayan Shekaru 11: Abubuwa 6 Game da Marigayi Tsohon Shugaban Najeriya

- ‘Yan Najeriya sun shiga shafukan sada zumunta domin tunawa da tsohon shugaban kasar, Alhaji Umaru Musa Yar’adua, shekaru 11 bayan rasuwarsa

- Yar’Adua haifaffen Katsina ya rasu yayin da yake kan karagar mulki bayan ya sha fama da rashin lafiya

- Har yanzu ‘yan Najeriya da dama na daukar marigayin dan siyasar a matsayin daya daga cikin shugabannin kwarai a tarihin kasar

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya mutu a rana irin ta yau shekaru 11 da suka gabata yayin da yake kan mulki.

Mutuwar tasa ta girgiza kasar sosai yayin da ake kallon ɗan siyasan wanda yake haifaffen Katsina a matsayin shugaba mai son zaman lafiya, tasiri, da gaskiya.

Har zuwa rasuwarsa, Yar'adua yayi fama da rashin lafiya wanda wasu makusantansa suka rufe, lamarin da ya haifar da tashin hankali a kasar a lokacin.

Yar'Adua Bayan Shekaru 11: Abubuwa 6 Game da Marigayi Tsohon Shugaban Najeriya
Yar'Adua Bayan Shekaru 11: Abubuwa 6 Game da Marigayi Tsohon Shugaban Najeriya Hoto: Thomas Lohnes/DDP/AFP
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Ya kamata Buhari Yayi Murabus Saboda Ya Gaza - Matasan Arewa

A shafukan sada zumunta, 'yan Najeriya suna tuna mutumin da mutane da yawa ke cewa da zai iya kawo sauyi matuka da yana raye don shugabantar kasar.

Don karrama shi, Legit.ng ta lissafa abubuwa shida game da marigayi shugaban na Najeriya a kasa:

1. An haifi Yar'adua a cikin garin Katsina; mahaifinsa, Musa Yar'Adua, shi ne ministan Legas a Jamhuriya ta Farko kuma ya rike sarautar Matawalle ta Masarautar Katsina, mukamin da 'Yar'adua ya gada daga baya.

2. ’Yar’Adua ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarar 1972 zuwa 1975, inda ya samu digiri na farko a kan ilmin kemistri, sannan ya dawo a 1978 ya ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin nazarin kimiyyar kemistri.

3. Nadin nasa shine karo na farko a tarihin Najeriya da aka zabi zababben shugaban farar hula ya mika mulki ga wani.

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abun da Ya Gani Game da Juyin Mulkin Shugaba Buhari

4. A matsayinsa na gwamnan jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007, ya mai da hankali kan ci gaban tattalin arziki na jiharsa, kuma an san shi da nuna sanin ya kamata a harkar kudi: ba wai kawai ya biya babban bashin jihar da ya gada ba, har ma ya tara rarar dala miliyan 50 a cikin baitul-malin.

5. A zaben shugaban kasa, wanda aka gudanar a ranar 21 ga Afrilun 2007, Yar'adua ya yi nasara da kashi 70% na kuri'un (kuri'u miliyan 24.6) bisa ga sakamakon da aka fitar a hukumance a ranar 23 ga Afrilu. Zaben ya kasance mai cike da ce-ce-ku-ce kuma Yar'adua da kansa ya amince da shi kuma ya yi alkawarin kawo gyara.

6. Bayan zaben, Yar'adua ya gabatar da gwamnatin hadin kan kasa. A karshen watan Yunin 2007, jam'iyyun adawa biyu, All Nigerian Peoples Party da Progressive Peoples Alliance suka amince su shiga gwamnatin 'Yar'Adua.

A gefe guda, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, a ranar Laraba, ya bayyana marigayi Shugaba Umaru Yar'adua a matsayin mutum mai hangen nesa.

Ya ce fatan Yar'adua shine samar da zaman lafiya da haɗa kan ƴan Nigeria.

Marigayi Ƴar'Adua ya rasu shekaru 11 da suka gabata a lokacin yana kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel