Rashin Imani: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah ana cikin Azumi

Rashin Imani: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah ana cikin Azumi

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun jefa mutane cikin jimami da alhini a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Idris Abubakar Sakaina a daren ranar Asabar, 8 ga watan Maris 2025
  • Tantiran ƴan bindigan sun hallaka matashin ne mai shekaru 32 a duniya a gaban gidansa da ke cikin birnin Ilorin, babban birnin jihar
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kwara, ta fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wa matashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Ƴan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.

Miyagun ƴan bindigan sun harbe Alhaji Idris Abubakar Sakaina ne a ranar Asabar, 8 ga watan Maris 2025.

'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Kwara
'Yan bindiga sun hallaka shugaban Miyetti Allah a Kwara Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke jami'an NDLEA a Kano, an gano laifinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah

Maharan dai sun tare shi a gaban gidansa da ke Oke Ose, cikin birnin Ilorin, sannan suka harbe shi har lahira.

Wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan ba su karɓi komai daga wajensa ba bayan sun kashe shi.

"Sun bar shi cikin jini. Ba su karɓi komai daga gare shi ba. Abin akwai mamaki kan dalilinsu na kai wannan harin."

- Wata majiya

Wata ganau mai suna Aina’u Sarki, ta ce bayyana cewa:

"Ina tare da shi mintuna 20 kafin a kashe shi. Wani ya kirani a waya ya shaida min cewa an harbe shi har lahira."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’ummomi daban-daban na ɓangaren Fulani, Muhammed Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Lahadi.

"Eh, an kashe shi a gaban gidansa da daddare a ranar Asabar. Maharan sun harbe shi sannan suka bar shi a nan."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Katsina duk da sulhun da aka yi da su

"A halin yanzu muna shirin jana’izarsa, amma ƴan sanda sun zo jiya sun fara bincike."

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kwara, Ejire-Adeyemi Toun, kan lamarin, sai ta ce za ta bayar da bayani daga baya.

Sai dai, har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton, ba ta yi hakan ba.

Marigayin, mai shekaru 32, tsohon mataimaki ne na musamman ga shugaban ƙaramar hukumar Moro, kuma jagoran matasan Fulani a jihar Kwara.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan sanda sun cafke ƴan bindiga a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta sanar da samun nasarar cafke wasu mutane guda huɗu da ake zargin ƴan bindiga ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa wurin ibada, sun yi garkuwa da babban limami da ɗalibi

Ƴan sandan sun cafke mutanen bayan sun shigo daga jihar Katsina domin siyan bindiga ƙirar AK-47 a cikin birnin Kano.

Bayan samun nasarar cafke waɗanda ake zargin, ƴan sandan sun kuma ƙwato kayayyaki masu yawa daga hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng