'Ya Isa,' Kungiyar Kasashen Musulmi Sama da 100 Sun Magantu kan Hare Haren Iran

'Ya Isa,' Kungiyar Kasashen Musulmi Sama da 100 Sun Magantu kan Hare Haren Iran

  • Ƙungiyar Haɗin Kan Kasashen Musulmi ta duniya (MWL) ta yi Allah-wadai da ci gaba da kai hare-hare kan ƙasashe uku
  • Shugaban kungiyar ya bayyana cewa hare-haren da kasar Iran ke kaiwa sun saɓa wa dokokin kasa da kasa da na addini
  • A daya bangaren, sojojin Jordan sun yi nasarar kakkabo wasu makamai masu linzami guda uku da aka harba kan iyakokinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia – Ƙungiyar Haɗin Kan Kasashen Musulmi (MWL) ta yi Allah-wadai da kakkausan harshe game da ci gaba da kai hare-haren Iran kan ƙasashen Kuwait, Bahrain, da kuma Jordan.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar a duniya, Dr. Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya sake jaddada Allah-wadai da waɗannan hare-hare.

Yadda aka yi taron kasashen Musulmi
Shugabannin kasashen Musulmi yayin wani taro a Uzbekistan. Hoto: Muslim World League
Source: Facebook

A sakon da MWL ta fitar a Facebook, Al-Issa ya ce hare-hare Iran sun saɓa wa dukkan koyarwar addini, dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa, kuma suna barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.

Kara karanta wannan

A karo na 3 a jere, Amurka ta kai munanan hare hare kan ƙasar musulunci ta Iran

Kasashen da abin ya shafa

Dr. Al-Issa ya bayyana cikakken goyon bayan ƙungiyar MWL ga ƙasashen Kuwait, Bahrain, da Jordan kan dukkan matakan da suke ɗauka domin kare kasarsu da lafiyar al'ummarsu.

A gefe guda kuma, dakarun tsaron ƙasar Jordan sun da cewa sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami guda uku na Iran da aka harbo zuwa yankunansu, inda suka ce babu wanda ya rasa ransa.

A halin da ake ciki, ƙasar Qatar ma ta fuskanci hare-haren sama, inda ma'aikatar tsaron ƙasar ta sanar da kakkabo wasu makaman, yayin da aka kunna kararrawar faɗakarwa a Bahrain.

Barazanar dakarun IRGC na Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun yi ikirarin kai hari kan dakarun Amurka da ke al-Tanf a kasar Siriya, a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da Amurka ta kai masu.

CNN ta wallafa cewa dakarun IRGC sun yi barazanar cewa muddin Amurka ta ci gaba da yin katsalandan a mashigar Hormuz, to babu digon man fetur ko na gas da za a bari a fitar daga yankin.

Kara karanta wannan

Rashin sani: Shaguben da sanatan Amurka ya yi ga Iran kwana 5 kafin ya mutu

Mutanen Iran na tafiya a kan hanya
'Yan Iran na wuce ta wajen da aka saka hoton Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, gwamnatin Amurka ba ta riga ta tabbatar da sahihancin harin da aka kai wa dakarun nata ba, yayin da ake fargabar yaɗuwar rikicin a yankin.

Amurka ta sayar wa Saudi makamai

A wani labarin na daban, mun kawo muku cewa Amurka ta amince da yarjejeniyar sayar wa ƙasar Saudiyya makamai na kusan dala biliyan 2.

Wannan mataki ya zo ne a ranar Laraba da nufin ƙarfafa garkuwar tsaron sararin samaniyar Saudiyya, musamman a daidai lokacin da takaddama tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ke ƙara ruruwa.

Hukumar ta bayyana cewa wannan ciniki zai taimaka wajen inganta tsaron ƙasar Saudiyya wadda ke taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin tekun Fasha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng