An kama jami'ar 'yan sanda da ta yi ciki ba tare da aure ba

An kama jami'ar 'yan sanda da ta yi ciki ba tare da aure ba

- Rundunar yan sandan Najeriya ta sallami wata jami'ar hukumar bisa daukar ciki ba tare da aure

- An kori jami'a Omolola da ke aiki a Iye Ekiti tare da umartar a kwace takardun ta na aiki da kuma tura bayanan ta IPPIS don datse albashin ta

- Laifin na ta ya sabawa sashe na 127 na dokar rundunar yan sandan ta kasa

Rundunar yan sandan Najeriya (NPF) ta kori wata mata mai mukamin kofur (corporal) mai suna Olajide Omolola bayan ta yi ciki kuma bata da aure, The Punch ta ruwaito.

A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar, hukumar yan sandan ta sanar korar jami'ar a wani sako da ya fito daga sashen kudi da tsare tsare na hukumar a Ado Ekiti.

An kama jami'an 'yan sanda da ta yi ciki ba tare da aure ba
An kama jami'an 'yan sanda da ta yi ciki ba tare da aure ba. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

An tura takardar ga DPOn Iye Ekiti inda Omolola ta ke da zama.

A cikin sakon, an umarci mai kula da harkokin kudi a Ekiti da ya tabbatar ya bada bayanan ga IPPIS don tabbatar da an dakatar da albashin ta.

"Sashe na 127 na dokar aikin yan sanda da ya hana mata yan sanda daukar ciki kafin aure na kunshe cikin takardar sallamar kofur Olajide Omolola wacce ta kammala makarantar horon yan sanda ranar 24/04/2020, " kamar yadda takardar ta nuna.

"An sallame ta daga aiki. A karbe duk wasu takardu nata da suka shafi aikin yan sanda nan take. Jami'in kudi na Ekiti. Zaka aika rahoto ga IPPIS Abuja don dakatar da albashin ta daga yanzu.

KU KARANTA: An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo

"Mataikan Kwamishinoni, da duk DPO na Ekiti. Ku fadakar da mata yan sanda illar laifin da gaggawa. "Omolola ta kammala makarantar horar da yan sanda 24 ga watan Afrilu, 2020, kuma an tura ta Iye Ekiti.

Sashe na 127 na aikin yan sanda na cewa, "duk jami'ar yan sanda mace da tayi ciki kafin auren ta a sallame ta daga aiki, kuma kar a sake daukar ta sai da sahalewar babban sufeto na kasa."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel