Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafin N6.6bn ga Yan Najeriya domin Rage Talauci

Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafin N6.6bn ga Yan Najeriya domin Rage Talauci

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ci gaba da raba tallafin kudi ga al'ummar Najeriya domin yaye masu kangin talauci da ake fama da shi
  • Majiyoyi sun ruwaito gwamnatin na cewa ta raba kimanin Naira biliyan 6.6 a karkashin shirin tallafin kudi na iyalai domin rage talauci
  • Ministan Harkokin Jin Kai, Bernard Doro, ya ce shirin zai taimaka wajen tallafa wa talakawa da inganta tattalin arzikin iyalai masu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana yadda ta raba biliyoyin kudi ga al'ummar kasa domin rage radadin talauci da ake ciki.

Gwamnatin ta ce ta raba kusan Naira biliyan 6.6 a jihar Imo karkashin shirin Tallafin Ci Gaban Iyalai da Karfafa Tattalin Arziki.

Gwamnatin Tinubu ta raba N6.6bn na tallafi
Shugaba Bola Tinubu da Ministan jin kai da walwala, Bernard Doro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a shafin Facebook inda ya yi bayani yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Owerri.

Kara karanta wannan

"Asiri zai tonu," Ana zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi ba

Musabbabin shirya ba da tallafin da aka yi

Ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne na gwamnati domin fitar da ‘yan Najeriya masu rauni daga kangin talauci.

A cewarsa, adadin mutanen da suka amfana da shirin ya kai 278,000, inda kowanne ya samu N75,000 a kashi uku.

Ya ce shirin na taimakawa iyalai wajen samun sauki da kuma damar shiga harkokin tattalin arziki mai dorewa.

Doro ya ce:

“Muna matukar godiya ga Shugaba Bola Tinubu saboda wannan shiri da ya shafi mafiya fama da talauci a cikin al’umma.”

Ministan ya kara da cewa kudaden ana tura su kai tsaye ga wadanda aka tantance ta hanyar rajistar jin kai ta kasa da lambar NIN, cewar Punch.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun bayyana godiya, suna cewa tallafin ya taimaka musu wajen farfado da kasuwancinsu.

Wata mai suna Chioma Nkwerre ta ce ta yi amfani da kudin wajen sake sayen kaya a shagon ta, wanda ya farfado da kasuwancinta.

Kara karanta wannan

Bayan yaudara na shekaru, Tinubu ya ƙaddamar da gyaran hanyar Gombe zuwa Maiduguri

An yabawa Gwamna Uzodinma kan ayyukan raya kasa
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo yayin taro a Owerri. Hoto: Hope Uzodinma.
Source: Twitter

An yabawa gwamna kan ayyukan raya kasa

Ministan ya kuma yabawa Gwamna Hope Uzodimma kan ci gaban da ake samu a jihar Imo.

Bernard Doro wanda aka nada a 2025 ya ce gwamnatin jihar ta nuna hadin kai mai kyau wajen aiwatar da shirye-shiryen jin kai na tarayya.

Uzodimma ya bayyana shirin a matsayin abokin hulda mai muhimmanci wajen rage talauci da inganta rayuwar al’umma.

Yake cewa jihar ta daidaita shirye-shiryenta da manufofin gwamnatin tarayya tare da kirkirar sahihin rajistar jin kai.

Gwamnan ya kuma yabawa sauyin tsarin biyan kudi kai tsaye zuwa asusun banki, yana mai cewa zai kara gaskiya da tsaro.

Ya ce matakin zai tabbatar da cewa tallafi yana kaiwa ga wadanda aka nufa kai tsaye ba tare da tangarda ba.

Tinubu ya raba miliyoyin kudi ga al'umma

A baya, an ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce ta raba tallafin kuɗi ga 'yan Najeriya sama da miliyan 34 domin rage radadin matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Umahi: Tinubu ya tattare manyan ayyukan tituna a Arewa

Ministan Jinƙai, Dr Bernard Doro, ya bayyana cewa ana sa ran kai tallafin zuwa miliyan 50 kafin ƙarshen shekarar 2026.

An kafa majalisar Jinƙai da Rage Talauci ta Ƙasa domin inganta haɗin gwiwa tsakanin tarayya, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.