Mummunan hatsarin mota ya lakume mutane 28 yan gida daya a jahar Bauchi

Mummunan hatsarin mota ya lakume mutane 28 yan gida daya a jahar Bauchi

Wasu mutane 28 yan gida daya sun mutu a sanadiyyar wani mummunan hadarin mota daya rutsa dasu a jahar Bauchi yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Yola na jahar Adamawa a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba.

Jaridar Punch ta ruwaito hadarin da ya auku a kan babban hanyar Bauchi zuwa Ningi ya yi muni matuka inda ya kona mutanen 28 kurmus, sai dai gawayinsu kadai aka iya tattarowa.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana alhininsa da mutuwar Sojoji 63 a hannun yan ta’adda

Da majiyar ta gana da wani dan uwan mamatan, kuma sakataren kungiyar yan jaridu reshen Arewa maso yamma, Abdullahi Yamadi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyanashi a matsayin lamari mai matukar bakanta rai.

“Da gaske ne lamarin ya faru, kuma dukkaninsu yan uwana ne, suna kan hanyarsu ta zuwa Yola a jahar Adamawa ne domin ziyarar yan uwa da abokan arziki a lokacin da hatsarin ya auku, ka san bayan an yi girbi mutane su kanyi amfani da wannan dama wajen tafiye tafiye.

“Sun fito ne daga Dutsanma ta jahar Katsina, suka shiga Jigawa, sun shiga Bauchi kenan motarsu ta yi gaba da gaba da wata mota dake tahowa, su 29 ne a cikin motar, dukkaninsu sun mutu, banda direba.” Inji shi.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto rundunar Yansandan jahar Bauchi bat ace uffan game da lamarin ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma gwamnatin kasar Nijar, tare da bayyana alhininsa bisa kisan da wasu gungun yan ta’adda suka yi ma dakarun Sojojin kasar Nijar guda 63 a garin Inates dake iyaka da kasar Mali.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, inda yace yan ta’addan sun fito ne daga kasar Mali, suka Nijar inda suka kashe Sojoji 63, ba’a san inda 34 suka shiga ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel