Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alhinin mutuwar babban malami Sheikh Isah Halliru

Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alhinin mutuwar babban malami Sheikh Isah Halliru

A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kebbi ta yi alhinin mutuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Haliru Abdullahi, wanda ya mutu yana da shekaru 117 a duniya.

A wani jawabi da Abubakar Dakingari, babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kebbi, ya fitar, ya ce Malamin ya mutu ne ranar Alhamis a Birnin Kebbi, bayan wata gajeriyar jinya.

A cewar Dakingari, gwaman jihar Kebbi, Abubakar Aiku Bagudu, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan mamacin.

Ya ce daya daga cikin 'ya'yan mamacin, Alhaj Samaila Dankasa, da kuma shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Alhaji Samaila Kamba, ne suka tarbi gwamna Bagudu yayin da kai ziyarar ta'aziyyar.

Gwamna Bagudu ya tuna wa jama'a cewa dukkan mai rai wata rana zai mutu, sannan ya yi addu'a Allah ya ji kan marigayin, ya gafarta masa tare da yi masa samako da Ajannatul Firdausi.

Alhaji Kamba ya yi wa gwamnan godiya bisa ziyarar da ya kai domin yi musu ta'aziyya.

Kafin rasuwarsa, marigayin shine Sarkin Zabarmawan Gwandu, mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa bisa yin kira ga zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin mutanen Najeriya da kasar Benin.

Ya mutu ya bar mata hudu, 'ya'ya 28 da jikoki 200 da 'ya'yan jikoki da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel