APC Ta Yi Shiri, Ta Fadi yadda Za Ta Lashe Zabe a dukkan Kananan Hukumomin Gombe
- APC ta bayyana kwarin gwiwar lashe dukkan kujerun zabukan kananan hukumomi da na kansiloli a zaben Gombe da za a gudanar ranar Asabar
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bai wa ‘yan takarar jam’iyyar goyon baya tare da yabawa ayyukan gwamnatin Gombe
- Gwamna Muhammadu Yahaya ya ce jam’iyyar za ta sake samun nasara saboda hadin kai, ayyuka da goyon bayan jama’a ga gwamnatin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gombe - Jam’iyyar APC ta bayyana kwarin gwiwar samun gagarumar nasara a zaben kananan hukumomi da za a gudanar ranar Asabar a jihar Gombe.
Jam’iyyar ta ce za ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli, bayan shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya amince da ‘yan takarar jam’iyyar tare da gabatar musu da tutocin takara.

Source: Twitter
Gwamna Yahaya ya yi alkawarin nasara
Da yake magana a wajen taron gabatar da tutocin ‘yan takarar APC a Gombe, Gwamna Muhammadu Yahaya ya ce jam’iyyar na shirin sake samun nasara a dukkan kananan hukumomin jihar 11, in ji rahoton Punch.
Yahaya ya bayyana APC a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a jihar, yana mai cewa karfinta ya samo asali ne daga hadin kai, ayyukan raya kasa da kuma goyon bayan jama’a.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar maimaita nasarorin zaben da muka samu tare da rike dukkan kujerun ciyamomi da na kansilo a karkashin APC. Karfinmu ya ta'allaka da hadin kanmu da amincewar jama’a da shugabancinmu.”
APC na son lashe kujerun ciyamomi
Gwamnan ya bayyana cewa APC na kokarin ci gaba da rike shugabancin dukkan kananan hukumomi da kujerun majalisu a jihar.
Ya ce jam’iyyar za ta kara karfafa shugabanci a matakin kasa ta hanyar aiki tare da kananan hukumomi 11 da kuma kananan hukumomin LCDA 13 da ke jihar.

Kara karanta wannan
Zargin bata suna: Kwankwaso ya yi barazanar kai malamin addini kotu, zai nemi N10bn
Yahaya ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar su kasance masu hadin kai tare da mayar da hankali wajen ganin APC ta samu nasara a zaben.
A yayin jawabin nasa, gwamnan ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa goyon bayan manyan ayyukan raya kasa a jihar Gombe, musamman babban aikin hanyar superhighway da ke ratsawa wasu sassan Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Shugaban APC ya yi magana
Ya ce aikin zai taimaka wajen inganta zirga-zirga, bunkasa kasuwanci da kuma saukaka rayuwar jama’a, cewar rahoton Independent.
A nasa bangaren, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yabawa Gwamna Yahaya kan ayyukan da ya ce sun taimaka wajen bunkasa jihar a fannoni daban-daban.
Yilwatda ya ce ziyarar da ya kai wasu yankuna, makarantu, jami’o’i, wuraren ayyukan hanya da cibiyoyin al’adu ta nuna cewa dimokuradiyya na samar da sauyi ga jama’a.
Ya kara da cewa mata ‘yan kasuwa, manoma da sauran mazauna jihar da ya gana da su sun nuna gamsuwa da yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da al’amuranta.
Tinubu ya hadu da dan takarar Gombe
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da dan takarar gwamnan APC a Gombe ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna ga Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ya taya dan takarar gwamnan murnar nasarar da ya samu a zaben fitar da gwani na APC da aka shirya kwanaki.
Asali: Legit.ng

