Ashura: An jibge 'yan sanda domin hana 'yan shi'a tattaki a jihar Kano

Ashura: An jibge 'yan sanda domin hana 'yan shi'a tattaki a jihar Kano

A yau 10 ga watan farko a shekarar Musulunci, ana sa ran mabiya kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a a Najeriya, za su gudanar da tattaki na tunawa da kuma nuna juyayin mutuwar Imam Hussaini ibn Ali, wanda aka kashe a yayin yakin Karbala shekaru fiye da dubu daya da suka gabata.

Ilahirin mabiya akidar shi'a a fadin duniya na gudanar da wannan tattaki domin nuna bakin cikin su a wannan rana ta 10 ga watan Al-Muharram, domin nuna bakin cikin a kan mutuwar Imam Hussain wanda ya kasance jikan Manzn Tsira, Annabi Muhammad (Salallahu Alaihi Wasallam).

A wani rahoto da muka samu daga jaridar The Punch, rundanar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta jibge fiye da jami'ai 200 a cikin birnin Kanon Dabo domin hana tattakin 'yan kungiyar shi'a, lamarin da ta ce ba za ta bari a gudanar da duk wani abu mai barazana ga zaman lafiya a kasar ba.

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya ce kwamishinan 'yan sandan Kano, Ahmed Iliyasu, ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama ya sabawa dokar haramta duk wani tattaki zai fuskanci fushin hukuma.

A wani rahoton da jaridar mu ta Legit.ng a kalato daga shafin Sahara Reporters, mun samu cewa a na yi mummunar arangama tsakanin jami'an tsaro da mabiyar akidar shi'a a jihar Kaduna, inda rayuka suka salwanta gami da jikkatar mutane da dama.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta hallaka yara 4 a garin Abuja

A na iya tuna cewa, a baya-bayan nan sufeto janar na 'yan sanda Muhammad Adamu, ya bayar da umarnin haramta duk wasu al'amura na kungiyar shi'a a Najeriya, lamarin da ya ce kungiyar haramtacciyar kuma ba za ta karbu ba a kasar.

A na ta bangaren, kungiyar shi'a cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin kakakin ta, Ibrahim Musa, ta ce babu gudu babu ja da baya akan gudanar da tattakin ta kamar yadda ta saba a kowace shekara, inda take cewa ba za a hana ta addini ba domin kuwa kundin tsarin mulkin kasa ya ba ta izini.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel