Hezbollah Ta Yi wa Sojojin Isra'ila Kwanton Bauna, Ta Ce Ta Hallaka da Dama

Hezbollah Ta Yi wa Sojojin Isra'ila Kwanton Bauna, Ta Ce Ta Hallaka da Dama

  • Kungiyar Hezbollah ta yi ikirarin kashewa da jikkata sojojin Isra'ila tare da lalata tankokin yaƙi uku kirar Merkava a Kudancin Lebanon
  • A daya bangaren kuma, sojojin Isra'ila sun tabbatar da mutuwar sojojin su huɗu, ciki har da kwamandan rundunar tankokin yaƙin da aka farmaka
  • Duk da cewa an yi sulhu da Amurka, hare-haren da Isra'ila ta kai a Kudancin Lebanon sun kashe mutane 24 tare da jikkata wasu da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lebanon - A ranar Juma'a, 19 ga Yunin 2026 Hezbollah ta yi iƙirarin cewa ta kashe tare da jikkata wasu sojojin Isra'ila da dama.

Bayan kashe sojoji, kungiyar ta ce ta lalata tankokin yaƙi uku a wani kwanton bauna da ta kai wa dakarun Isra'ila a Kudancin Lebanon.

Kara karanta wannan

Mataimakin Trump ya yi tone tone kan Isra'ila, ya gargadi jami'an Netanyahu

Sojojin Isra'ila a Lebanon
Wasu sojojin Isra'ila a iyakar kasar Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda aka kashe sojojin Isra'ila

Rahoton Anadolu Agency ya ce kungiyar Hezbollah ta ce mayaƙanta sun sa ido kan wata rundunar Isra'ila da ta ƙunshi tawagar tankokin yaƙi da kuma tawagar sojojin ƙasa da ke ƙoƙarin matsawa zuwa Arewacin tsaunukan Ali al-Taher.

Mayaƙan Hebollah sun harba tankokin yaƙi uku kirar Merkava da makamai masu linzami, inda suka lalata su tare da cinna masu wuta kafin daga bisani su kai hare-hare masu tsanani da rokoki da manyan bindigogi kan rundunar.

Ƙungiyar ta ce an ci gaba da fafatawa bayan kwanton baunar, amma ba ta bayar da cikakkun bayanai kan asarar rayuka ba.

A wata sanarwa da ta biyo baya, Hezbollah ta ce wata rundunar Isra'ila ta sake ƙoƙarin kwashe gawawwaki da sojojin da suka jikkata a ƙarƙashin hayaki mai yawa, yayin da take harba makamai da dama.

Ƙungiyar ta ce ta kai wa rundunar hari da rokoki da kuma bama-bamai, tana mai iƙirarin cewa hare-haren sun isa kai tsaye wajen da aka nufa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe maza 2, an sace mutum 17 ciki har da matan aure a Sokoto

Hezbollah ta ce an gudanar da hare-haren ne domin kare Lebanon da al'ummarta, da kuma mayar da martani ga abin da ta kira keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ke yi.

Bayanin sojojin Isra'ila

Tun da farko, sojojin Isra'ila sun ce sojoji huɗu, ciki har da kwamandan rundunar tankokin yaƙi, sun mutu jim kaɗan bayan da aka kai wa tankarsu hari.

Sun ce an kai harin yayin da suke aiki tare da wata rundunar yaƙi ƙarƙashin jagorancin Givati Brigade a kusa da ƙauyen Manteef da ke Kudancin Lebanon.

Sojan Isra'ila da aka kashe
Wajen jana'izar sojan Isra'ila da aka kashe a Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wani bangaren, BBC ta rahoto cewa sojojin Isra'ila sun kai hare-haren sama masu yawa kan ƙauyuka da garuruwa a Kudancin Lebanon da asubahin ranar, lamarin da ya kashe mutane 24 tare da jikkata wasu.

Amurka ta gargadi Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa Donald Trump, JD Vance ya gargadi shugabannin Isra'ila kan sukar kasar shi.

Vance ya yi magana ne bayan wasu jami'an gwamnatin Benjamin Netanyahu sun fara sukar Trump kan sulhu da ya yi da kasar Iran.

Ya kara da cewa Amurka ce babbar mai taimakon Isra'ila, musamman a bangaren makamai saboda haka bai kamata su rika sukar ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng