Wata Sabuwa: Iran Ta Yi Watsi da Tattaunawa da Amurka kan Makamai Masu Linzami

Wata Sabuwa: Iran Ta Yi Watsi da Tattaunawa da Amurka kan Makamai Masu Linzami

  • Iran ta bayyana cewa shirinta na makamai masu linzami ba zai kasance cikin duk wata tattaunawa da Amurka nan gaba ba
  • Sabuwar yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma ta mayar da hankali ne kan shirin nukiliya da sassauta takunkumin tattalin arziki
  • Birnin Tehran ya jaddada cewa tana kera makamai masu linzami ne domin kare ƙasar Iran, kuma ba batun da za a tattauna a kansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Gwamnatin Iran ta bayyana cewa shirinta na makamai masu linzami ba zai kasance cikin batutuwan da za a tattauna da Amurka ba a nan gaba.

Iran ta bayyana hakan ne duk da sabuwar yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka cimma domin kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

Idan ta dage cewa ba za a tattauna batun mallakar makaman nukiliyarta ba
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Aragchi (dama). Hoto: Valentin Flauraud / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta yi matsaya kan karfin makamanta

Wannan na zuwa ne bayan shugabannin Amurka da Iran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ke shimfiɗa hanya ga ƙarin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da kuma sassauta wasu takunkuman tattalin arziki, in ji rahoton The New York Times.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce ƙasar ba za ta amince a tattauna kan ƙarfinta na kariya ba.

A wata hira da gidan talabijin na gwamnatin Iran, ya bayyana cewa makamai masu linzamin ƙasar ba su cikin abubuwan da za a iya sanya su a teburin sulhu.

Ya ce:

"Makaman Iran an tanade su ne domin kariya da amfani a filin daga, ba domin tattaunawa ba."

- Esmaeil Baqaei.

Donald Trump ya sassauta matsayarsa

A wani sabon salo ne aka ji Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba zai zama abin adalci ba idan aka hana Iran mallakar wasu makamai masu linzami yayin da sauran ƙasashe ke da su.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya amince Iran ta mallaki makamai masu karfin gaske

Trump ya ce akwai bambanci tsakanin makamai masu linzami da kuma shirye-shiryen ƙera makaman nukiliya, yana mai jaddada cewa babban abin da ke damun Amurka shi ne tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

Sabuwar matsayar ta nuna cewa har yanzu akwai muhimman batutuwa da za su ci gaba da jawo muhawara tsakanin Tehran da Washington duk da yarjejeniyar da suka cimma.

Trump ya dawo ya ce ba zai zama abin adalci ba a hana Iran mallakar makamai masu linzami.
Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan yarjejeniya da Iran a ranar Alhamis. Hoto: Kevin Dietsch/Getty Images
Source: Getty Images

Bangaren da yarjejeniyar ta fi shafa

Sabuwar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Washington da Tehran ta fi mayar da hankali kan shirin nukiliyar Iran da kuma hanyoyin rage takunkuman da aka kakaba mata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sai dai babu wani sashe a yarjejeniyar da ya yi magana kai tsaye kan shirin makamai masu linzami, batun da Amurka da Isra'ila suka dade suna nuna damuwa a kai.

Idan ba a manta ba, a lokacin da rikicin ya shiga kwanaki 40, wuraren adana makamai da cibiyoyin tsaron Iran sun fuskanci hare-hare daga Amurka da Isra'ila.

Duk da haka, Iran ta ci gaba da mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi zuwa wurare daban-daban a yankin.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar ci gaba da kai hari Iran duk da cimma yarjejeniya

Sulhun Iran da Amurka ya fusata Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Isra’ilawa daga bangarori daban-daban sun nuna fushi kan yarjejeniyar farko tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan ƙasar suna kallonta a matsayin barazana ga tsaron Isra’ila yayin da ake tsaka da yaki.

Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce zai ci gaba da hana Iran mallakar makamin nukiliya, ko da yarjejeniya ta tabbata ko ta rushe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com