'Yan Haramtacciyar Kungiyar IPOB Sun Budewa Sojoji Wuta, Jami'an Najeriya Sun Mutu

'Yan Haramtacciyar Kungiyar IPOB Sun Budewa Sojoji Wuta, Jami'an Najeriya Sun Mutu

  • A yau ne rundunar sojojin kasar nan ta rasa jami'anta a jihar Abia bayan 'yan haramtacciyar kungiyar IPOB sun kai musu mummunan hari
  • Yau 30 ga watan Yuni ne kungiyar take bikin ranar kafa kasar Biafra da ake yi duk shekara, tare da umartar dukkanin mazauna kudu maso gabas su zauna a gida
  • 'Yan ta'addar kimanin 15 ne suka kai harin, sannan sun kona motoci, sai dai har yanzu rundunar sojojin kasar nan ba ta ce uffan a kan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Abia - Rundunar sojojin Najeriya ta yi gagarumar asara bayan mambobin haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB dake rajin kafa kasar Biafra ta kai musu hari.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

Yau ne ranar da 'yan kungiyar ke bikin tunawa da kasar da suke neman kirkira tare da ballewa daga Najeriya, inda suka umarci dukkanin mazauna kudu maso gabas su zauna a gida.

Sojojin Najeriya
'Yan ta'addan IPOB sun kashe sojoji 4 a Abia Hoto:@HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Harin 'yan IPOB a jihar Abia

Premium Times ta wallafa cewa yan ta'addar sun kashe sojoji guda hudu, tare da kona ababen hawa da dama a harin na yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan ta’addar kimanin su 15 ne suka kai harin a wurin duba ababen hawa da ke kwanar Obikabia da misalin karfe 8.00 na safe.

Wani da abin ya faru a kan idonsa, Marvelous ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun rufe fuskokinsu sannan suka budewa sojojin wuta.

‘Yan ta’addan IPOB sun kona motoci

‘Yan haramtacciyar kungiyar IPOB masu rajin warewa daga Najeriya sun kai hari kan sojojin Najeriya a safiyar yau.

Kara karanta wannan

'Abin kunya': NBA ta soki Lauyoyi da Masu shari'a kan dambarwar masarautar Kano

Rahotanni na cewa wani soja guda daya ya samu raunuka, yayin da ‘yan ta’addar suka kona ababen hawa, kamar yadda Sahara reporters ta wallafa.

Wani shaidan gani da ido, Marvellous ya shaidawa manema labarai cewa mutanen gari da dama sun samu raunuka a harin.

Duk da munin harin da ‘yan ta’addan IPOB suka kai kan sojojin kasar nan a jihar Abia, har yanzu rundunar sojojin kasar nan ba ta ce komai kan batun ba.

'Dan ta'adda ya mika wuya a Kaduna

A baya mun kawo muku labarin cewa wani kasungurmin dan ta'adda da ya addabi al'umma ya zubar da makamansa tare da mika wuya ga jami'an tsaro.

Hatsabibin dan ta'addan mai suna Lawal Kwalba ya kai kansa wurin sojoji a Kaduna wanda ya biyo bayan hare-haren da jami'an ke kaiwa kan 'yan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel