IPOB Ta Gargadi Tinubu Kan Ta’addancin Kungiyar, Ta Kalubalance Shi a Kotu

IPOB Ta Gargadi Tinubu Kan Ta’addancin Kungiyar, Ta Kalubalance Shi a Kotu

  • Kungiyar rajin kafa kasar Biafra, IPOB ta gargadi shugaban kasa, Bola Tinubu da ya cire su a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda
  • Mai Shari’a, Abdul Kafarati a ranar 20 ga watan Satumban 2017 ya ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda
  • Kungiyar ta tura gargadin ne yayin da ta ke neman a cire sunanta matsayin ‘yar ta’adda ko kuma su hadu a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Kungiyar IPOB ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da ya cire sunanta a matsayin ‘yan ta’adda ko kuma ya fuskanci shari’a.

Wannan na zuwa ne bayan Mai Shari’a, Abdul Kafarati ya ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ta’addanci a ranar 20 ga watan Satumban 2017, Legit ta tattaro.

Kungiyar IPOB ta kalubalanci Tinubu a kotu, ta yi masa gargadi
IPOB ta nemi Tinubu ya kare kansa a kotu. Hoto: IPOB.
Asali: Twitter

Meye kungiyar IPOB ke cewa kan Tinubu?

Kungiyar ta bayyana haka ne a yau Juma’a 27 ga watan Oktoba ta bakin kakakinta, Emma Powerful, Tori News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Za a Biya Nnamdi Kanu Naira Biliyan 8 Bayan Kotu Ta Soke Haramcin Kungiyar IPOB

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emma ya ce Gwamnatin Tarayya ta gagara zuwa ta kare kanta a gaban kotun daukaka kara kan wannan mataki na gwamnatin.

Ya ce sun daukaka kara kan wannan mataki na kotun tun shekarar 2018 wanda kwararrun lauyoyin kungiyar su ka jagoranta.

Ya kara da cewa sai dai gwamnatin na kara bata lokaci kan shari’ar don kawai ta kawo cikas kan shari’ar da ake yi.

Wane gargadi kungiyar IPOB ta yi wa Tinubu?

Ya ce:

“Tun bayan daukaka kara da kungiyar IPOB ta yi, Gwamnatin Tarayya da alkalan da su ka siya sun gagara samun zama da lauyoyinmu.
“Gwamnatin da alkalansu na tsoron ganawa da lauyoyinmu yayin da mu ke jiransu a kotun don ci gaba daga inda aka tsaya a shari’ar.”

Ya ce kungiyar wacce mai girma, Mazi Nnamdi Kanu ke jagoranta na mamakin yadda Gwamnatin Tarayya ke gudun kare kansu a kotun, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Kotu ta yi hukunci kan IPOB, za ta biya Kanu

A wani labarin, babbar kotun da ke zamanta a jihar Enugu ta soke haramcin da aka yi wa ‘yan IPOB a matsayin ‘yan ta’adda.

Babban alkalin kotun, A O Onovo shi ya yanke hukuncin inda ya ce hakan ya saba kundin tsarin mulki a kasar.

Ya ce wannan hukunci da aka dauka a shekarar 2017 ya ci karo da tsarin mulki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel