'Yan Bindigan da Suka Sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga Sun Turo Saƙo a Katsina
- Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga sun nemi kuɗin fansa
- Wani daga cikin ƴan uwansa wanda ya nemi a sakaya sunnasa ya ce maharan sun tuntuɓe su, kuma sun nemi Naira miliyan 250
- Har yanzu dai babu wani ci gaba daga jami'an tsaro game da ƙoƙarin ceto tsohon sojan, wanda aka sace ranar Laraba da daddare
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - 'Yan bindigar da suka sace tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa kasa hidima watau NYSC, Manjo-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) sun kira waya.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa kafin su sake shi.

Asali: Facebook
Wata majiya daga iyalansa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigar sun tuntuɓe su.

Kara karanta wannan
Janar Tsiga: Mutane sun shiga firgici sakamakon sace tsohon shugaban NYSC a Katsina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, masu garkuwa da Maharazu Tsiga sun faɗa masu cewa suna neman Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa.
Yadda aka sace Janar Maharazu Tsiga
An ce maharan sun yi garkuwa da Birgediya Janar Tsiga mai ritaya tare da wasu mutum tara a garin da kuma wasu ƙauyukan maƙota.
Rahotanni sun bayyana cewa fiye da 'yan bindiga 100 ne suka mamaye gidansa da misalin karfe 12:30 na dare ranar Laraba.
An ce da zuwansu suka karya ƙofar gidan, suka fara ɓarna har sai da tsohon janar din ya fito ya tambaye su abin da suke nema, suka tafi da shi.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Bakori/Danja a jihar Katsina, Abdullahi Balarabe Dabai, ya tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kewaye gidan gaba daya kafin su sace shi.
Babu wani ƙarin bayani daga jami'an tsaro
Har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoto, ba wani bayani daga sojoji ko 'yan sanda dangane da kokarin ceto tsohon janar din daga hannun miyagun.
Babu wani tabbaci ko gwamnati ko iyalansa za su iya biyan kudin fansa, amma ana sa ran jami'an tsaro za su dauki matakin ceto shi da sauran wadanda aka sace.
Wani mazaunin Tsiga da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa Legit Hausa cewa maharan sun tuntuɓi iyalan tsohon shugaban NYSC.
Ya ce mutane ke ta yaɗa adadin kuɗin fansar da aka nema amma su iyalan sun ƙi yin ƙarin bayani kan lamarin, alamu sun nuna suna ƙoƙarin ɓoye lamarin saboda yanayin tsaro.
"Eh gaskiya ne an kira iyalansa mun samu tabbaci amma abin ba a bayyana shi ga kowa saboda yanayin tsato, muna fatan dai Allah ya dawo mana da shi gida lafiya," in ji mutumin.
Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu ba
A baya, kun ji cewa gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya jaddada cewa ba zai nemi sulhu da ƴan bindiga ba.
Gwamnan ya ce rangwamen da zai iya yi wa ƴan ta'adda shi ne idan sun yi tubar gaskiya da gaskiya, amma ba zai taɓa yin sulhu da su ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng