Ana Shari’a da Diezani Alison-Madueke a Kotu, Sunan Ministan Buhari Ya Fito

Ana Shari’a da Diezani Alison-Madueke a Kotu, Sunan Ministan Buhari Ya Fito

  • Akwai yiwuwar Emmanuel Ibe Kachikwu zai yi shari’a da hukuma a kan zargin karbar rashawa
  • Ana zargin mutanen Diezani Alison-Madueke sun ba tsohon ministan man cin hanci a shekarar 2015
  • Ibe Kachikwu ya rike shugabancin kamfanin NNPC bayan Muhammadu Buhari ya karbi mulki

United Kingdom - Emmanuel Ibe Kachikwu wanda ya yi minista a Najeriya, zai iya samun kan shi a matsala yayin da sunan shi ya fito a shari'a.

Wani rahoto da The Cable ta kadaita da shi ya bayyana cewa an bankado sunan Emmanuel Ibe Kachikwu wajen binciken Diezani Alison-Madueke.

Madam Diezani Alison-Madueke ta rike kujerar ministan man fetur tsakanin 2010 da 2015, yanzu haka ana kararta a kotu kan zargin karbar cin hanci.

Kachikwu da Diezani Alison-Madueke.
Tsofaffin ministocin fetur Emmanuel Ibe Kachikwu da Diezani Alison-Madueke Hoto: Diezani Alison-Madueke, Ibe Kachikwu
Asali: Facebook

Diezani Alison-Madueke ta karbi rashawa?

Lauyoyi su na tuhumar tsohuwar ministar da karbar rashawar kudi, kayan alatu, kadarori da yawo a manyan jiragen sama domin bada kwangila.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashin Tashoshi Ya Zarce N720

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta ce akwai wasu manyan jami’an da su ka yi wa gwamnatin Najeriya aiki da ake zargin akwai hannunsu a badakalar da ake bincike a kotu.

Sunayen wadanda aka samu sun hada da Ibe Kachikwu, fitaccen attajiri, Benedict Peters da tsohon shugaban kamfanin PPMC, Haruna Momoh.

Wasu ‘yan Najeriyan da ke cikin wadanda ake tuhuma tare da tsohuwar ministar a kotu sun hada da Olatimbo Bukola Ayinde da Fasto Doye Agama.

Ibe Kachikwu ya musanya zargin

Rahoton ya ce ana zargin Olatimbo Bukola Ayinde ya ba Ibe Kachikwu cin hanci a watan Agustan 2015 domin ya iya samun gindin zama a wajensa.

A lokacin da ake zargin abin ya faru, Kachikwu ya na matsayin shugaban kamfanin mai na NNPC. Kachikwu ya fitar da jawbai, musanya zargin nan.

Idan har an yi haka, wannan ya sabawa sassa na 6 da 11 na dokar hana cin hanci da rashawa ta shekarar 2010, kuma kotun Birtaniyar za ta yi hukunci.

Kara karanta wannan

Za a Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21 a Kan Mutuwar Mohbad

Badakalar takardun Bola Tinubu

Dokar kasa ta hana wanda aka samu da takardar shaidar bogi tsayawa takarar shugaban kasa, ku na da labari ana zargin Bola Tinubu da wannan.

Bangaren Atiku Abubakar su na ikirarin Shugaban kasa ya gabatarwa INEC da diflomar bogi saboda haka su ke neman kotun koli ta tunbuke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel