Hukumar EFCC Ta Shiga Yin Gwanjo da Wasu Kadarorin Diezani Alison-Madueke

Hukumar EFCC Ta Shiga Yin Gwanjo da Wasu Kadarorin Diezani Alison-Madueke

  • EFCC ta shirya yin gwanjo da kadarorin wasu ‘yan siyasa da ‘yan kasuwan da aka samu da laifin sata
  • Kadarorin da za a sa a kasuwa su na Legas, Ribas, Abuja, Anambra, Gombe, Ebonyi, Kaduna, dsr
  • Mai sha’awar mallakar kayan zai je shafin EFCC ya samu fam, daga nan zai je ya ga kayan da idonsa

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa tayi kira ga mutane su nemi sayen kayan da gwamnati ta karbe.

A karshen makon nan Daily Trust ta rahoto cewa kayan da gwamnatin tarayya ta karbe su na garuruwan Legas, Ribas, Anambra, Gombe da Delta.

Har ila yau an karbe kaya daga ‘yan siyasa daga ‘yan kasuwa a jihohin Ebonyi, Kaduna, Delta, Edo, Kwara, Kuros Riba, Osun, Oyo da birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

Ana zargin daga cikin kaya da kadarorin da aka karbe a biranen Abuja, Legas da Fatakwal na tsohuwar Ministar fetur, Diezani Alison-Madueke ce.

Gidaje 23 sun shiga kasuwa

Hukumar EFCC ta na tuhumar Diezani Alison-Madueke da mallakar wadannan kaya ta haramtacciyar hanya. Tun 2015 ake shari’a da 'yar siyasar a kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya nuna a unguwar Banana Island da ke Legas, katafaran gidaje 23 aka karbe a hannun Allison-Madueke wanda tayi Minista a mulkin PDP.

Diezani Alison-Madueke
Tsohuwar Ministar fetur, Diezani Alison-Madueke Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani jawabi da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba 2022, hukumar EFCC ta ce mutane da kamfanonin da suke sha’awar kayan za su iya sayensu.

Akwai sharadin mallakar kayan

Daga sharudan da aka bada shi ne ya zama hukumar ba ta taba samun mutum da laifi ba. Za a iya samun labarin nan a jaridar Aminiya ta ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3

Duk wani wanda aka taba daurewa a baya a dalilin aikata laifi, bai cikin wadanda za su samu damar sayen wadannan kadarori da ake shirin yin gwajonsu.

Masu neman ayi masa gwanjon za su iya sauke fam daga shafin yanar gizo na hukumar (watau www.efcc.gov.ng), bayan nan sai su dirje kayayyakin.

Kadarorin nan sun hada da wani gida mai dakuna uku da sashen samari a rukunin gidaje na Foreshore a titin Onikoyi da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

EFCC v Diezani Alison-Madueke

Tun a karshen shekarar bara, aka samu rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen sa kadarori da dukiyoyin wasu ‘yan siyasa a kasuwa.

Alison-Madueke wanda ta rike Ministar harkokin man fetur da Ministar sufuri tsakanin 2007 zuwa 2015, tana cikin wadanda za ayi gwanjon kayan ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel