Najeriya Ta Yi Kafar Talabijin Mai Tashoshi 100 da za a Rika Kallo Kyauta
- Najeriya ta ƙaddamar da FreeTV, wani dandali na talabijin na zamani da zai bai wa gidaje damar kallon tashoshi sama da 100 kyauta
- Rahotanni sun nuna cewa sabon dandalin zai samar da tashoshin labarai, wasanni, fina-finai, kide-kide da shirye-shirye don yada ilimi
- Gwamnatin Tarayya ta ce FreeTV wani ɓangare ne na shirin sauya tsarin watsa shirye-shiryen talabijin daga tsarin gargajiya zuwa zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da FreeTV, wani dandali na talabijin na ƙasa wanda zai samar da tashoshi sama da 100 a faɗin ƙasar nan.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa za a rika kallon tashoshin ne kyauta ba tare da biyan kuɗin wata-wata ba.

Source: Facebook
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa a X cewa an ƙaddamar da dandalin ne a ranar Laraba, 17 ga Yuni, 2026, a matsayin wani ɓangare na shirin sauya tsarin watsa shirye-shiryen talabijin.
Tashar talabiji FreeTV da aka kafa
A cikin wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar, an bayyana cewa FreeTV zai samar wa ‘yan Najeriya da tashoshin labarai na ƙasa, yankuna da jihohi, wasanni, fina-finai da kiɗe-kide.
Bugu da kari, sanarwar ta ce za a samar da tashoshin yada ilimi, na yara, da kuma tashoshin harsunan gida da suka haɗa da Yarbanci, Hausa da Igbo.
Za a samu damar kallon FreeTV ta tauraron dan adam, ta hanyar watsa shirye-shiryen ƙasa da kuma manhajar FreeTV ta wayar hannu, wanda zai bai wa masu kallo a birane da karkara damar cin gajiyarsa.
Yadda za a kalli tashohin talabijin
Arise News ta wallafa cewa Najeriya ta ce ba za a buƙaci ‘yan Najeriya su sayi sababbin talabijin ba kafin samun damar kallo a sababbin tashoshin.
Talabijin da ake da su yanzu za su iya amfani da FreeTV idan suna da na’urorin da suka dace da tsarin DVB-T2 ko DVB-S2, yayin da wasu gidaje da ke da na’urorin free-to-air za su iya amfani da wannan sabis ɗin kai tsaye.

Source: Facebook
Bayanin Shugaban hukumar NBC
Da yake magana kan ƙaddamar da FreeTV, shugaban NBC, Charles Ebuebu, ya ce ƙaddamar da dandalin ya tallafa wa burin gwamnati na faɗaɗa fasaha a ƙasar da kuma bunƙasa kirkire-kirkire a Najeriya.
Charles Ebuebu ya ce FreeTV za ta samar wa iyalai shirye-shiryen talabijin kyauta ba tare da biyan kuɗin wata-wata ba, tare da buɗe sababbin hanyoyin watsa shirye-shirye ga 'yan Najeriya.
Ya kuma ce za a inganta ɓangaren watsa shirye-shirye da nishaɗi na Najeriya ta hanyar samar da cibiyoyin samar da shirye-shirye na yankuna a Legas, Abuja, Fatakwal, Enugu, Kano da Benin
An raba tallafin noma a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da shirin rabon tallafin kayan noma a damunar bana.
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa an kaddamar da shirin ne domin ba manoma kayan aikin da za su kara samar da abinci.
Rahotanni sun nuna cewa an rage kudin takin zamani da kaso mai tsoka ga manoma a kusan dukkan yankunan Najeriya a karkashin shirin.
Asali: Legit.ng

