Dandalin Kannywood: Ina so infi mahaifi na suna a harkar fim - Ahmad Ali Nuhu
- Ina so infi mahaifi na suna a harkar fim - Ahmad Ali Nuhu
- Ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da wata mujallar fim
- Ahmad Ali Nuhu din da ya fara fitowa a talabijin tun yana dan shekara biyar a duniya
Dan fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa a masana'antar fim watau Ali Nuhu mai suna Ahmad ya bayyana cewa yana da burin duniya ta san shi fiye da mahaifin sa a harkar.
KU KARANTA: Yan shi'a sun kada 'yan sanda a kotun garin Sokoto
Ahmad Ali Nuhu din dai ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da wata mujallar fim a watannin baya inda ya ce yana da burin ya fi mahaifin nasa suna da kuma daukaka a harkar ta shirya fina-finan Hausa.
Legit.ng ta samu cewa Ahmad Ali Nuhu din da ya fara fitowa a talabijin tun yana dan shekara biyar a duniya ya bayyana haka zalika ya bayyana cewa yana iya taka duk rawar da aka saka shi yayi a cikin fim yanzu haka dai-dai gwargwado.
Daga karshe kuma yaron jarumin ya yi wa masoyan sa da ma dukkan masu sha'awar fina-finan Hausa fatan alheri da kuma godiya tare kuma da rokon su rika basu shawara a duk inda suka ga ba dai-dai ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng