Gwamnatin Tinubu na Shirin Kara Haraji kan Kudin Kiran Waya da Fetur? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamnatin Tarayya ta karyata rahotanni da ke nuna cewa ta amince da ƙarin haraji kan harkokin sadarwa da man fetur
- Ta bayyana cewa shawarwarinda asusun ba da lamuni (IMF) ya bada ba manufofin Najeriya ba ne kuma ba dole a aiwatar da su ba
- Gwamnatin ta tabbatar da cewa har yanzu rangwamen VAT kan fetur yana nan, yayin da aka soke harajin excise kan harkokin sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa ta amince ko kuma tana shirin ƙaƙaba sababbin haraji kan harkokin sadarwa da kayayyakin man fetur.
An fara yada labarin cewa za a kara kakaba haraji kan harkokin sadarwa da suka shafi kiran waya, data da tura sakonni bayan fitar rahoto kan tattalin arzikin Najeriya na Asusun Lamuni na Duniya (IMF).

Kara karanta wannan
Duk da matsin da ake ciki, ana tunanin kara kudin kira da tura saƙonnin waya a Najeriya

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta tattaro cewa wasu rahotanni sun danganta wa IMF cewa Najeriya na iya buƙatar faɗaɗa harajin VAT zuwa kan fetur tare da ƙaƙaba haraji kan harkokin sadarwa.
Gwamnati na shirin kara haraji a Najeriya?
Sai dai a wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na Ma’aikatar Kuɗi, Efe Ovuakporie, ya fitar a ranar Laraba, gwamnatin ta karyata jita-jitar da ake yadawa.
Sanarwar ta ce rahoton IMF ya ƙunshi nazarin da asusun ya yi kan tattalin arzikin ƙasar da kuma shawarwarin da ya gabatar domin gwamnati ta yi la’akari da su.
Ta ce waɗannan shawarwari ba su zama manufofin gwamnati kai tsaye ba, kuma ba dole ne Najeriya ta aiwatar da su ba.
“Batutuwan da suka shafi haraji ana yanke hukunci a kansu ne ta hanyoyin doka da kundin tsarin mulki ya tanada, tare da la’akari da bukatun ƙasa da yanayin tattalin arziki da ake ciki,” in ji sanarwar.
An cire harajin VAT daga fetur
Gwamnatin ta bayyana cewa har yanzu rangwamen harajin VAT da aka yi wa kayayyakin man fetur yana nan daram kuma ba a soke shi ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito
Ta kuma yi bayanin cewa duk da cewa dokoki sun tanadi yiwuwar ƙaƙaba wani ƙarin kuɗi kan man fetur, hakan ba zai fara aiki ba sai an fitar da umarnin minista tare da wallafa shi a jaridar gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
“Babu wani irin tsari makamancin haka da ake nazari a kai a halin yanzu,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ce dakatar da waɗannan kuɗaɗe ya taimaka wajen rage tasirin tashin farashin makamashi a duniya ga gidaje da kasuwanci, tare da taimakawa wajen daidaita farashin man fetur a cikin ƙasa.
An soke harajin sadarwa
Haka kuma gwamnatin ta ce harajin excise da aka ƙaƙaba kan harkokin sadarwa kafin shekarar 2023 an soke shi ƙarƙashin sababbin dokokin haraji, saboda haka ba ya aiki a yanzu.
Saboda haka, gwamnatin ta ce rahotannin da ke cewa ana shirin ƙaƙaba haraji kan harkokin sadarwa ko fetur ba gaskiya ba ne kuma ya kamata jama'a su yi watsi da su.
NCC na duba yiwuwar kara kudin sadarwa
An ji cewa hukumar NCC a Najeriya ta fara nazari kan batun kara kudin haɗa hanyoyin sadarwa tsakanin kamfanonin waya da ke aiki a kaar nan.
kuɗin haɗa hanyoyin sadarwa, wanda ake kira Mobile Termination Rate (MTR), shi ne kuɗin da wata hanyar sadarwa ke biya wa wata idan abokin cinikinta ya kira lambar wata hanyar daban.
Wannan tsari ne da ke tabbatar da cewa masu amfani da layukan waya a Najeriya za su iya sadarwa da juna duk da kasancewarsu a hanyoyin sadarwa mabambanta
Asali: Legit.ng

