Duk da Matsin da Ake ciki, Ana Tunanin Kara Kudin Kira da Tura Saƙonnin Waya a Najeriya
- Hukumar NCC a Najeriya ta fara nazari kan batun kara kudin haɗa hanyoyin sadarwa tsakanin kamfanonin waya
- Hakan ya biyo bayan shafe shekaru ba tare da daukar matakin ba, lamarin da ka iya janyo ƙarin kuɗin kira da saƙonnin waya
- Masana sun ce hauhawar farashi, sauyin darajar Naira, tsadar makamashi da kayan aiki sun ƙara wa kamfanonin sadarwa nauyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta fara nazarin kuɗin haɗa hanyoyin sadarwa tsakanin kamfanonin waya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an dauki matakin ne musamman saboda kira da saƙonnin SMS.

Source: UGC
Daily Trust ta ruwaito cewa kuɗin haɗa hanyoyin sadarwa, wanda ake kira Mobile Termination Rate (MTR), shi ne kuɗin da wata hanyar sadarwa ke biya wa wata idan abokin cinikinta ya kira lambar wata hanyar daban.
Yawan kudin kira da ake biya a Najeriya
Wannan tsari ne da ke tabbatar da cewa masu amfani da layukan waya a Najeriya za su iya sadarwa da juna duk da kasancewarsu a hanyoyin sadarwa mabambanta.
Ana cajin tsakanin N3.90 zuwa N4.70 kan kowane minti ta kira, idan aka ƙara wannan kuɗi bayan nazarin, masu amfani da waya za su iya fuskantar ƙarin kuɗin kira da SMS.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan ƙayyade kuɗin MTR a Legas, abokin hulɗa a kamfanin KPMG, Mista Wole Adenekan, ya ce ƙananan kuɗaɗe na iya hana kamfanoni saka jari a bangaren sadarwa.
Ya bayyana cewa kuɗin da ya dace da ainihin farashi yana ƙarfafa zuba jari mai inganci tare da taimakawa bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Source: Facebook
Matsalar da matakin ka iya jawowa
A cewarsa, idan aka saita MTR ba daidai ba, manyan kamfanoni za su iya takura ƙananan masu fama ta hanyar ƙirƙirar shingayen shiga kasuwa.
Adenekan ya kuma ce ƙarin kuɗin haɗa hanyoyin sadarwa da ya wuce kima kan koma kan masu amfani ta hanyar tsadar farashin ayyukan sadarwa, cewar Punch.
Ya ce raguwar darajar Naira, hauhawar farashi da ƙarin kuɗin makamashi da kayan aiki tun daga shekarar 2018 sun sauya tsarin kashe kuɗin kamfanonin sadarwa sosai.
Ya ƙara da cewa yaɗuwar fasahar 5G da amfani da AI da IoT suna sauya yadda ake amfani da hanyoyin sadarwa da kuma yadda ake gudanar da ayyuka.
Har ila yau, ya ce kamfanonin OTT suna karɓar kaso mai yawa na kira da saƙonni, lamarin da ke rage dogaro da tsohon tsarin haɗa hanyoyin sadarwa.
A jawabinta na maraba, shugabar sashen gasa da farashi na Hukumar NCC, Omotayo Mohammed, ta ce wannan nazari wani muhimmin mataki ne na tattalin arziki domin daidaita dokokin hukumar da canje-canjen da ke faruwa a fannin sadarwa.
Basukan da aka ci a MTN, GLO
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun bayyana cewa masu amfani da layukan waya a sun ci bashin kati na kusan tiriliyoyin Naira a shekarar 2025.
Afirka ta bayar da sama da 94% na duk bashin kati da kamfanin ya raba, lamarin da ya nuna karuwar matsin tattalin arziki.
Karuwar bashin kati da kananan rance sun taimaka wajen habakar kudaden shiga duk da karin hadarin rashin biya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

