Shekaru 24 da mutuwar Abiola, ‘Dan Marigayin ya roki Gwamnati ta binciki abin da ya faru

Shekaru 24 da mutuwar Abiola, ‘Dan Marigayin ya roki Gwamnati ta binciki abin da ya faru

  • Abdul Abiola ya fito yana kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya binciki mutuwar mahaifinsu
  • Yaron marigayin ya kuma roki gwamnatin tarayya ta gano wadanda suka hallaka Kudirat Abiola
  • MKO Abiola ya mutu ne yayin da yake tsare a kurkuku ana tsakar maganar shirin fito da shi a 1998

Daya daga cikin ‘ya ‘yan Marigayi MKO Abiola, ya yi kira na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari ya binciki mutuwar mahaifinsu da mai dakinsa.

Jaridar Premium Times ta ce Abdul Abiola ya yi wannan kira a shafinsa na Twitter, @AbdulMKO.

Da yake magana a ranar Talata, 4 ga watan Mayu 2022, Abdul Abiola ya bayyana cewa akwai bukatar mutane su san abin da ya kashe Cif MKO Abiola.

Abdul Abiola ya bukaci shugaban kasa watau Mai girma Muhammadu Buhari ya bankado tarihin abin da duk ya faru bayan soke zaben da aka yi a 1993.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

This Day ta ce matashin ya kuma bukaci ayi bincike kan mutuwar Kudirat Abiola, ya na ganin yin hakan zai sa gwamnatin Najeriya ta tabbatar da adalci.

MKO Abiola
Marigayi MKO Abiola Hoto: highprofile.com.ng
Asali: Getty Images

Abin da Abdul MKO ya fada

“Lokaci ya yi da mutanen Najeriya za su san gaskiyar abin da ya faru bayan zaben 12 ga watan Yuni na 1993.”
“Tare da kuma gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwar MKO Abiola da Kudirat Abiola da sauran ‘yan mazan jiya.”
“Ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kakkabe kayan ajiya na tarihi domin a wanzar da adalci.”

Abin da ya faru a 1993

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa MKO Abiola ne yake daf da samun nasara a zaben shugaban kasa na Yunin 1993 da Janar Ibrahim Babangida ya shirya.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

Kwatsam sai aka ji Janar Babangida ya soke wannan zaben karfin a kammala tattara kuri’u, hakan ya hana a tabbatar da nasarar Abiola a jam’iyyar SDP.

IBB dai ya mika mulki ga gwamnatin rikon kwaryar da Janar Sani Abacha ya hambarar da ita. Daga bisani sai Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaba.

Wannan abin ne ya sa aka kama Cif Abiola har aka daure shi. Ana shirin fito da Attajirin a watan Yulin 1998 sai ya yi wata mutuwa mai matukar ban mamaki.

Najeriya sai Bello

Kwanaki aka ji cewa wata Ɗiyar MKO Abiola, Hafsah Abiola ta karɓi shugabancin yaƙin neman zaɓen Yahaya Bello a matsayin shugaban Najeriya a 2023.

Hafsat Abiola ta ce ta yi nazari ta gano babu wani wanda zai iya gyara Najeriya da ya zarce Bello. A gefe guda kuma wasu 'yanuwan na ta su na wata jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel