Kamfanin NNPCL Ya Sauya Farashin Mai saboda Yakin Iran da Amurka

Kamfanin NNPCL Ya Sauya Farashin Mai saboda Yakin Iran da Amurka

  • Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara farashin danyen mai da ya ke sayarwa kasashe saboda yakin Iran da Amurka a Gabas ta Tsakiya
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa karin farashin zai fara aiki ne daga kayan da aka yi oda a watan Mayun 2026
  • Masani a harkar makamashi a Najeriya, Farfesa Adeola Adenikinju ya yi karin bayani game da yadda karin farashin zai shafi jama'ar kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara farashin danyen mai na Najeriya da ake fitarwa, inda dokar za ta fara aiki daga farkon watan Mayun 2026.

Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da rufe hanyar ruwan Hormuz duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Tehran.

Kara karanta wannan

OPEC+: UAE ta dauki mataki 1 da ya girgiza Saudiyya da kasuwar mai ta duniya

Shugaban NNPCL, Bayo Bashir Ojulari
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari na jawabi a Abuja. Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da karin farashin ne a wani sako da shafi mai sharhi kan farashin man fetur na Oil Price ya wallafa.

Najeriya ta kara farashin mai

Rahoto ya ce Najeriya na amfana da yakin Amurka da Iran, inda NNPCL ya kara farashin shahararren danyen mai na Bonny Light da $6.13 kan kowace ganga idan aka kwatanta da watan Afrilun 2026.

Haka kuma, an kara farashin Forcados da $7.01 kan kowace ganga. Wannan na iya nuna cewa matatar Dangote za ta biya karin kudi wajen sayen danyen mai, wanda a karshe zai iya janyo karin farashin man fetur.

Rahoton ya bayyana cewa:

“Najeriya na cin gajiyar yakin Iran. Kamfanin NNPC ya kara farashin danyen mai da yake sayarwa, zai fara aiwatar da haka a watan Mayu.”

An kuma ruwaito cewa farashin Bonny Light ya kai $124.86 kan kowace ganga a ranar Talata, sakamakon karin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya. Kudin ya fi farashin Brent na duniya da kusan $14, wanda shi ma ya haura $110.

Kara karanta wannan

Jirgin Rasha ya kutsa cikin ruwan da Amurka ta jibge sojoji ta hana wucewa

Mashigar Hormuz da Iran ta toshe
Mashigar Hormuz da aka toshe ta dagula kasuwar makamashi a duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farashin Brent ya kai $110 yayin da masana ke gargadin cewa yakin Amurka da Iran na iya rikidewa zuwa rikici mai tsawo.

Bayanin masani kan kudin mai

Tsohon shugaban kungiyar masana tattalin arzikin makamashi ta Najeriya, Farfesa Adeola Adenikinju, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “takobi mai kaifi biyu” ga Najeriya.

Masanin ya bayyana cewa Najeriya za ta samu karin kudin shiga, amma kuma wahalar rayuwa za ta kara tsananta kan jama’ar kasa.

Punch ta wallafa cewa ya ce karin farashin fetur ya janyo hauhawar kudin sufuri da kuma hauhawar farashin sauran abubuwa, wanda ke kara nauyi ga talakawa.

UAE za ta fita daga OPEC +

A wani labarin, kun ji cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da cewa za ta fice daga kungiyar OPEC da OPEC+ a wata mai zuwa, bayan kusan shekaru 60 tana cikinta.

Kasar ta ce wannan mataki zai taimaka mata wajen biyan bukatar makamashi ta duniya a nan gaba, bayan zuba jari da ta yi domin kara yawan samar da mai.

Ana kallon ficewar a matsayin babban kalubale ga kungiyar OPEC, wadda ke da tasiri sosai wajen sarrafa yawan mai da kuma farashinsa a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng