An Shiga Tashin Hankali da 'Yan Ta'addar Lakurawa Suka Kashe Sojojin Najeriya 5

An Shiga Tashin Hankali da 'Yan Ta'addar Lakurawa Suka Kashe Sojojin Najeriya 5

  • Sojoji biyar sun mutu yayin da aka yi wata arangama tsakanin sojoji da 'yan ta'addar Lakurawa a yankin Gudu da ke Sokoto
  • Rundunar sojojin Najeriya ta ce duk da asarar jami'anta, ta kashe 'yan ta'addar shida tare da kwace bindigogi da harsasai 160
  • Sojoji sun nemi jama’a su kasance masu sanya ido, su kuma sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Sojoji biyar sun mutu yayin wani samame na haɗin gwiwa kan ƴan ta'addan Lakurawa a karamar hukumar Gudu ta Jihar Sokoto.

Kakakin rundunar hadin gwiwa karkashin Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Sojoji sun yi magana yayin da 'ayn ta'addar Lakurawa suka kashe sojoji 5 a Sokoto
Sokoto: 'Yan ta'addar Lakurawa sun kashe sojoji 5 a wata arangama. Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Lakurawa sun kashe sojojin Najeriya 5

Laftanal Abubakar ya ce sojojin hedikwatar tsaro na musamman sun kashe ƴan ta'adda shida yayin artabu mai tsanani a lokacin samamen, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Duk da nasarar da aka samu, wannan aiki ya zo da babban rashi, inda sojoji biyar masu jarunta suka rasa rayukansu."

Sai dai Laftanal Abubakar ya ce sojojin sun kwace bindigogin AK-47 huɗu, harsasai 160 kirar 7.62mm, da kuma kwankon harsasai kirar 12.7mm guda ɗaya.

Sojoji sun nemi taimakon al'ummar Gudu

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu sanya ido a cikin al’ummominsu tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Hukumomin tsaro sun ce goyon bayan jama'a yana da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a garuruwansu.

Rahoton Punch ya nuna cewa an yi kira ga al'ummar yankin Gudu da kewaye da su taimaka wa sojoji ta hanyar bayar da bayanai masu amfani don yakar ta'addanci.

Karanta wasu labarai da suka shafi Lakurawa

Lakurawa sun yi karfi a Sokoto, suna karbar zakka, sun yiwa al'umma gargadi

Kara karanta wannan

Sojoji 22 sun rasu bayan kashe Boko Haram 70 a wani kazamin fada

An samu karin bayani kan 'yan ta'addar Lakurawa da suka shigo Arewa

Asalin Lakurawa da shirin da sojojin Najeriya suka yi na kawo karshen 'yan ta'addan

Lakurawa: Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda na raba miliyoyi domin rudar matasan Arewa

Yadda Lakurawa ke sauya limami a Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza, Gazali Aliyu, ya ce kungiyar Lakuwa ta dauki lokaci mai tsawo a jihar Sokoto.

Gazali ya ce ƴan ta'addan Lakurawa sun yi kaurin suna yanzu inda har suke barazana ga 'yan bindiga a kan su bi su ko su bar yankin.

Ya bayyana yadda ƴan ta'addan ke ƙara yawa, ya tabbatar cewa farko ba su wuce mutane 50 ba, amma yanzu har suna sauke limamai su nada wadanda suke so.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.