NSCDC ta kama shugaban kungiyar miyagu ta Shila a Adamawa

NSCDC ta kama shugaban kungiyar miyagu ta Shila a Adamawa

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen jihar Adamawa ta kama hatsabibin shugaban kungiyar Miyagu ta Shila, Micheal Linus.

Mr Nuradeen Abdullahi, Kwamandan Rundunar ta jihar ya gabatar wa manema labarai wanda ake zargin a ranar Talata a Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Abdullahi ya ce rundunar ta hanyar tattara bayanin sirri ta kama Linus da aka fi sani da Damudu, shugaban kungiyar miyagu ta Shila da wasu miyagun biyu da rundunar ta dade tana nema.

Kwamandan ya yi bayanin cewa kafin kama shi, Linus gawurtaccen wanda ake zargi da aikata laifi ne da ya kasance yana fitinar mutanen jihar.

NSCDC ta kama shugaban kungiyar Shilla a Adamawa
Jami'an NSCDC. Hoto daga Premiumtimes Ng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

"Mun dade muna neman Micheal Linus, mai shekara 22. Ya kware wurin aikata laifuka karkashin kungiyar Shila, koyar da kananan yara miyagun ayyuka da sayar da muggan kwayoyi.

"Bayanan da muke da shi sun nuna cewa wanda ake zargin ya yi wa mutane da dama rauni a jihar.

"Sauran wadanda ake zargi da laifin sun hada da, Mohammed, mai shekara 33, dan kwangilar bogi da ya kware wurin zuwa makarantun gwamnati a kauyuka yana gabatar da kansa a matsayin dan kwangila.

"Ya kware wurin satar rufin gidaje. Ya kan rudi yan kauyen cewa an bashi kwangilar canja rufin makarantu idan ya cire sai ya tafi ya siyar, " in ji Abdullahi.

Ya ce na ukun kuma wani Mustapha Ismail ne da ake zarginsa da satar motocci da kayan mutane.

Asirin Abdullahi ta tonu ne lokacin da aka kama shi yana kokarin kwace wa wani mota kuma aka karbo motar.

A wani labari mai alaka da wannan, ya ce rundunar a baya bayan nan ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da aikata laifuka daban daban a karamar hukumar Yola ta Kudu.

Abdullahi ya ce an kama wadanda ake zargin ne bisa aikata laifuka da suka hada da sata, shiga gidajen mutane ba da izini ba da damfara ta intanet.

"Ana cigaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu cikin aikata laifin, da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel