Bauchi: EFCC Ta Sake Gurfanar da Akanta Janar a gaban Kotu kan Badakalar N1.48bn

Bauchi: EFCC Ta Sake Gurfanar da Akanta Janar a gaban Kotu kan Badakalar N1.48bn

  • Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sirajo Jaja, tare da wasu da ake zargi da karkatar da kudin jama'a a gaban kotu
  • Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati tana zargin Jaja da hada kai da wasu wajen aika Naira biliyan 1.48 zuwa asusun wani kamfani
  • Yanzu haka, hukumar tarayyar na neman karin wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifuffuka da dama da suka hada da halasta kudin haram

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta sake gurfanar da Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sirajo Jaja, a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan zargin hannu a badakalar kudade da suka kai Naira biliyan 1.48.

EFCC na binciken jami'in gwamnatin Bauchi
EFCC ta ci gaba da shari'a da Akanta Janar a Bauchi @SenBalaMohammed, @officialEFCC
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa an gurfanar da Jaja ne a gaban mai shari’a Obiora Egwuatu, tare da wani mai hada-hadar canji Aliyu Abubakar da kamfaninsa mai suna Jasfad Resources Enterprise.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC na zargin Akanta Janar da almundahana

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa hukumar EFCC na zargin mutanen da ta kai kotu da laifuffuka guda biyar da suka hada da halatta kudin haram karkatar da kudin jama’a zuwa aljihunsu.

A baya dai, hukumar ta EFCC ta gurfanar da su a gaban kotu a ranar 7 ga Afrilu bisa wasu laifuffuka tara, inda ake zarginsu da karkatar da Naira biliyan 8.38.

Sai dai a wannan karon, EFCC ta rage yawan zarge-zargen da kuma adadin kudin da ake zargin sun yi sama da fadi da su daga baitul mali.

Hukumar EFCC na shari'a da jami'an Bauchi
Akanta Janar ya musanta zargin karkatar da kudin Bauchi Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

A cewar sababbin tuhumar da ake yi masu, EFCC ta zarge su da cire sama da Naira biliyan 1.19 daga asusun gwamnati zuwa asusun kamfanin Jasfad a tsakanin Oktoba zuwa Disamba 2024.

A wata tuhuma daban, an kuma zargesu da karkatar da Naira miliyan 296 tsakanin Janairu zuwa Maris 2025 daga baitul malin jihar zuwa asusun kamfanin.

Mutanen da EFCC ke tuhuma a Bauchi

Hukumar EFCC ta ambaci wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a badakalar da suka hada da Abubakar Muhammed Hafiz, Ari Manga da Muhammed Aminu Bose.

Har yanzu, hukumar na nemansu ruwa da jallo, yayin da wadanda aka gurfanar a gaban kotu suka musanta laifuffukan da ake tuhumar su da aikatawa.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma, Gordy Uche da Chris Uche, sun roki kotu da ta bar su ci gaba da da cin moriyar belin da aka ba su a baya, kotun ta kuma amince da rokon.

EFCC na zargin Akanta Janar da wawashe N8.38bn

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar EFCC ta gurfanar da Babban Akanta na Jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, a gaban kotu kan zargin karkatar da kudin gwamnati har Naira biliyan 8.38.

An gurfanar da Jaja tare da wani mai gudanar da harkar canjin kudi, Aliyu Abubakar, da kamfaninsa Jasfad Resources Enterprise, a gaban mai shari’a O.A. Egwuatu.

A cewar EFCC, an gurfanar da su bisa tuhume-tuhume tara da suka shafi halasta kudin haram, karkatar da dukiyar jama’a da kuma almundahanar kudin daga asusun gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.