Yanzu-Yanzu: EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Badakalar N70bn

Yanzu-Yanzu: EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Badakalar N70bn

  • Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rasha ta EFCC ya ce suna binciken gwamnan Zamfara Bello Matawalle
  • Abdulrashid Bawa ya yi wannan bayani ne ta bakin daraktan kula da harkokin jama’a na hukumar
  • Ya ce hukumar ba ruwanta da ko kai Fasto ne ko Limami idan ka aikata laifin da ya saba doka shikenan

Abuja- Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce tana binciken gwamnan jihar Zamfara¸ Bello Matawalle bisa zargin sama da fadi har na N70bn.

Hukumar har ila yau ta ce tsohon ministan wuta Sale Mamman da aka kama ‘yan kwanakinnan kan zargin sama da fadin N22bn yana tsare har yanzu.

Bello Matawalle/Zamfara
EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Kan Badakalar N70bn. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Shugaban hukumar Abdulrashid Bawa ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu inda ya ce kada ‘yan Najeriya su damu da maganan da gwamnan ya yi dangane da yadda hukumar ke aiwatar da ayyukanta, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Zugo Hukumar EFCC Ta Binciki Duka Mukarraban Gwamnatin Buhari

Gwamnan ya zargi Bawa kan yadda yake nuna wariya a binciken EFCC, ya kuma kalubalanci hukumar EFCC da ta binciki mukarraban gwamnatin shugaba Buhari ba gwamnoni kadai ba, jaridar Daily Trust ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bawa ya maida martani

Bawa wanda ya yi magana ta bakin daraktan kula da harkokin jama’a na EFCC, Osita Nwajah ya ce hukumar bai kamata ta mutunta gwamnan da martani ba, kawai ta yi ne don fayyace komai.

A cewarsa:

“Abin burgewa ne yadda Matawalle ke son zama shugaba wanda zai fada wa EFCC wanda za ta bincika. A wannan hali ‘barawo’ ne zai ce kada a taba shi sai an kama sauran ‘barayi’?
“Abin takaici ne yadda Matawalle zai bai wa EFCC umarnin wanda za su kama, wadanda ake zargi da suke hannun hukumar mu sun fito daga kowane bangare na al’umma.”

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

Waye EFCC ke kamawa?

Ya kara da cewa:

“Samun cancantar shiga komar hukumar shi ne idan ka aikata laifi, ba ruwanmu ko kai Fasto ne ko Limami, gwamna ko minista.
“A yanzu haka, tsohon ministan wuta yana hannunmu kan badakalar N22bn, wannan bai jawo hankalin Matawalle ba.”

Gwamna Matawalle Ya Dawo Da Sarkin da ya Bai Wa Dan Bindiga Sarauta a Zamfara

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya dawo da sarautar Alhaji Aliyu Garba rawaninsa a matsayin sarkin Yandoto.

Gwamnan ya shekaran bara ya dakatar da sarkin bisa zargin bai wa dan bindiga sarauta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel