Father Mbaka da Buhari: ’Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Fitaccen Faston, Sun Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Father Mbaka da Buhari: ’Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Fitaccen Faston, Sun Caccaki Fadar Shugaban Kasa

- Kwanan nan ne fadar Shugaban kasa ta zargi Father Mbaka da neman tukwici bayan ya goyi bayan Shugaba Buhari a 2015

- Zargin ya zo ne bayan malamin ya nemi shugaban kasar da ya yi murabus ko kuma a tsige shi kan halin da kasa ke ciki

- ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayinsu game da lamarin kuma wasu sun nuna goyon bayansu ga malamin yayin da wasu ke adawa da shi

Shahararren fasto dinnan, Father Mbaka, ya ja hankali sosai biyo bayan abin da ya faru kwanan nan akan shi.

Lamarin ya fara ne lokacin da malamin addinin ya yi kira ga tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari idan ya gaza yin murabus saboda karuwar rashin tsaro a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: An Shiga Rudani Yayinda Gwamnan APC Ya Caccaki INEC a Kan Sanar da Ranakun Zaben 2023

Father Mbaka da Buhari: ’Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Fitaccen Faston, Sun Caccaki Fadar Shugaban Kasa
Father Mbaka da Buhari: ’Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Fitaccen Faston, Sun Caccaki Fadar Shugaban Kasa Hoto: Rev Fr Ejike Camillus Mbaka Adoration Ministry AMEN
Asali: Facebook

Mbaka wanda ya goyi bayan Buhari a lokacin zaben shugaban kasa na shekarar 2015, ya bayyana karara cewa bai ji dadin wannan gwamnati ba kamar yadda ya zargi shugaban kasar da “yin shiru” duk da yawan kashe-kashe a Najeriya.

A cikin wani abu mai ban mamaki, fadar shugaban kasa ta amsa kuma ta buɗe wasu abubuwa game da malamin.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, a cikin wata sanarwa ta Facebook a ranar Juma'a, 30 ga Afrilu, ya yi ikirarin cewa malamin ya taba neman kwangila a matsayin tukwici saboda goyon bayan Buhari sau biyu wajen lashe shugabancin kasar.

A cewar Shehu, Buhari ya ki yarda kuma hakan ya sa Mbaka ya juya baya kuma a yanzu yake caccakar gwamnati mai ci.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashesu, Gwamna Umahi Yana Neman Sulhu

Wannan fallasar ta zo wa wasu ‘yan Najeriya a ba-zata. Yayin da wasu ke da ra'ayin cewa gwamnatin na kokarin bata sunan malamin ne kawai, wasu kuma sun bayyana Mbaka a matsayin mai son wuce gona da iri.

Legit.ng ta tattaro wasu daga martanin da yan Najeriya suka yi game da rigimar Mbaka da Buhari.

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu

Ga tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, malami da fadar shugaban kasa ba su cancanci a mayar da hankali a gare su ba.

Henry Shield ya ce ba za a amince da kazafi ba a kan malamin.

Sodiq ya ce duk wani hari da aka kai wa Mbaka, to hari ne kan kudu.

@MrJoshuaSampson ya bayyana:

"Shin gaskiyar cewa Mbaka ya je zawarcin kwangila ya kawar da batun rashin tsaro? Shin wannan ne ya sa ake fama da rashin tsaro? Ni da nake ta kira ga Shugaban kasa da ya magance rashin tsaro, yan kwangila nawa na kai Aso Rock? Mbaka ya riga ya kunyata kansa, babu buƙata! "

@TheoAbuAgada ya ce:

"Ba lallai ne mu so Father Mbaka ba amma wannan ɗabi'ar ta bata suna da zagin waɗanda ke sukan shugaban ƙasar ta hannun mataimakansa abun tashin hankali ne."

A gefe guda, Yekini Nabena, mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya ce Ejike Mbaka, Shugaban cocin Adoration Ministry, Enugu, (AMEN) yana yi wa gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari barazana, The Cable ta ruwaito.

Nabena ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke martani kan kalaman da aka ce babban malamin addinin kiristan ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel