Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gyara a Tsarin Imprest, Ta Rage Kudin da Ake ba Ministoci a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta kayyade adadin kudin da kowane minista zai iya karba a tsarin Imprest domin biyan bukatunsu na yau da kullum
- Hakan na kunshe ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele
- A cewar sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Yuni, 2026, ministoci za su iya karɓar mafi girman adadi na N700,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta bullo da sababbin matakai domin ƙarfafa bin doka da oda wajen sarrafa kuɗaɗe a ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati.
Sababbin dokokin sun haɗa da kayyade adadin kuɗin jami'an gwamnati za su iya karba a tsarin imprest tare da ƙara sa ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati.

Source: Twitter
Mene ne kudin imprest da ake ba ministoci?
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gyare gyren da aka yi na ƙunshe ne a cikin takardar 2026 Annual General Imprest Warrant da Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya sanya wa hannu.
Tuni dai Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar da sanarwar aiwatar da tsarin ba da kudin a hukumance.
Imrest kuɗi ne da ake bayarwa ga jami'an gwamnati don biyan kuɗaɗen bukatun yau da kullun da na gaggawa waɗanda ƙila ba sa buƙatar cikakken tsarin gwamnati.
Sauye-sauyen gwamnatin tarayya ta yi
A cewar sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Yuni, 2026, ministoci za su iya karɓar mafi girman adadi na N700,000 a karkashin wannan tsari, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Sai kuma manyan sakatarorin da daraktoci na ma'aikatun tarayya za su samu N500,000, yayin da shugabannin hukumomi da sassan gwamnati kuwa za su iya karɓar N300,000.
Haka zalika shugabannin ofisoshi a jihohi da sauran jami'an gwamnatin tarayya da suka cancanta a ba au wadannan kudi za su samun akalla N100,000.
Gwamnati ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da tanade-tanaden Financial Regulation 1003, kuma yana daga cikin ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa dukiyar al’umma.

Kara karanta wannan
Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno
Haka kuma, gwamnati ta takaita yawan lokutan da za a iya mayar da kuɗin domin sake karɓar wani. Sabuwar dokar ta ce za a yi hakan sau ɗaya a watanni uku, kuma ba zai wuce sau biyu ba idan akwai buƙatar gaggawa.

Source: Facebook
Ofishin Akanta Janar ya kuma umurci dukkan hukumomin gwamnati masu gudanar da asusun kansu da su gabatar da rahoto cikin kwanaki 30, wanda zai nuna yadda aka rufe asusun imprest na 2025 da jerin sunayen waɗanda aka amince su karbi 2026.
An kuma wajabta wa masu karbar imprest buɗe asusun banki na musamman domin gudanar da kuɗaɗen, tare da aika rahoton wata-wata kan yadda aka kashe kuɗin da kuma hujjojin mayar da bayanan kashe kuɗin.
An kara wa ma'aikata alawus a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da biyan karin alawus na musamman na kashi 40 cikin 100 ga ma’aikatan gwamnati a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa an cimma matsayar ne bayan wani dogon zama da Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Esther Walson-Jack.
Hukumar Kula da Albashi da Kudin Shiga ta Kasa (NSIWC) ta fitar da takardar aiwatar da sabon alawus din.
Asali: Legit.ng
