Yaron da Ya Mutu Ya Dawo Sarai Yayin da Ake Hidimar a Coci a Majami’ar Apostle Suleman

Yaron da Ya Mutu Ya Dawo Sarai Yayin da Ake Hidimar a Coci a Majami’ar Apostle Suleman

  • Wani lamari mai ban mamaki ya faru yayin da fasto ya tada wani yaron da aka ce ya riga ya mutu a asibiti
  • Mahaifin yaron ya kawo shi coci, an yi nasarar ceto masa dansa, lamarin da ya ba mutane mamaki sosai
  • An yada bidiyon abin da ya faru da kuma yadda coci ya shiga jazamar ibada bayan ganin lamari mai ban mamaki

Benin - Ana kyautata zaton wani yaron da ya mutu ya dawo a yayin da ake hidimar addu'ar coci a birnin Benin.

Wannan lamari ya faru ne a wani taron addu'a da malamin coci Apostle Johnson Suleman ke gudanarwa mai taken Mighty Turnaround a birnin na Benin.

Suleman, wanda kuma shine mu'assasin Omega Fire Ministries Worldwide ya shiga mamaki yayin da mahaifin yaron ya bayyana masa abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Wannan lamari dai ya fara fita ne daga bakin wani mutum da aka ce ma'aikaci ne a wannan cocin.

Yaron da ya mutu ya tashi ya ba da mamaki a coci
Yaron da Ya Mutu Ya Dawo Sarai Yayin da Ake Hidimar a Coci a Majami’ar Apostle Suleman | Hoto: Johnson Suleman
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"A kawo yaron nan a mace da safen nan. Yayin da kake addu'a ga marasa lafiya, ya kwantar da yaron a kasa sai ya daura hannunsa akan mataccen yaron. Bayan ka yi addu'a, yaron ya farfado."

Da yake karin haske tare da godiya ga abin da ya faru, mahaifin yaron ya ce:

"Godiya ga uban gida Almasihu. Sunana fasto David Oshoken. Da safen na da misalin karfe 3 na safe, matata ta kira ne lamarin da na ya yi muni, cewa na zo na asibiti.
"Yayin da na isa asibiti, nan da nan na dauko da na. Na kudurra cewa, matukar baba yana nan, to babu abin da zai sami da na. Ya riga ya yi sanyi.

Kara karanta wannan

Satar turaren N4,000 ya sa kotu ta yi fushi, ta yankewa matashi wani hukunci mai ban mamaki

"Na kawo da na. Na kawo shi dandamali na kwantar dashi. Dole baba ya ga da na. Bayan yin addu'a, kawai sai ya dawo a raye."

An yada bidiyon lokacin da ake bayyana abin da ya faru a cocin.

Kalli bidiyon:

A wani labarin kuma, wani fasto ya caccaki jama'ar da ke halartar cocinsa bisa laifin kin siya masa agogo mai tsada.

Faston da ya dage tare da yin maganganu marasa dadi kan mabiyansa, inda ya kira su fatararru masara anini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel